Amurka ta sanar da kammala janye sojojinta da kayan aiki daga sansaninta na karshe a Jamhuriyar Nijar.
“Ma’aikatar Tsaro ta Amurka da Ma’aikatar Tsaron Kasa ta Jamhuriyar Nijar sun sanar da kammala janyewar dakarun Amurka daga sansanin sojin sama na 201 da ke Agadas,” in ji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.
- Zanga-zangar Birtaniya: Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ‘Yan NijeriyaÂ
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace
Amurka ta ce tun ranar 19 ga Mayu 2024 ta fara kokarin janye dakarunta daga kasar ta Yammacin Afirka da ke karkashin mulkin soji, kuma Amurka da dakarun sojin Nijar za su ci gaba da aiki a makonni masu zuwa don tabbatar da komai ya tafi kamar yadda aka tsara.
Pentagon ta ce Amurka ta inganta sansanin sojin saman Nijar na 201 da ke kusa da garin Agadas a tsakiyar kasar, da manufar habaka dangantakar tsaro da dakarun sojin Nijar da kokarin yaki da ta’addanci a yankin.
Sanarwar ta ce “A sama da shekaru goman da suka gabata, dakarun Amurka sun horar da dakarun Nijar tare da taimakawa a yaki da ‘yan ta’adda na IS da Al Qaeda a yankin.”
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin sojin Nijar ta bukaci Amurka ta bar kasar sakamakon tabarbarewar alakarsu bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.
Amurka ta ce cikakken hadin kai da sadarwa tsakaninta da dundunar sojin Nijar sun tabbatar da an kammala kashe sojojin kamar yadda aka tsara ba tare da samun wata tangarda ba.
Dukkanin bangarorin sun bayyana irin “sadaukarwar da dakarun kasashen biyu suka nuna,” in ji sanarwar.