Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa waɗanda ke cin gajiyar shigo da mai za su yi iya ƙoƙarinsu wajen daƙile ci gaban da matatar man Ɗangote ta samu a Nijeriya.
Obasanjo, ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Financial Times, inda ya siffanta matatar man Dangote, a matsayin wani ci gaba da ya kamata ya ƙarfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da ma waɗanda ba ‘yan Nijeriya ba.
Tofa albarkacin Obasanjo, na zuwa ne daidai lokacin da shugaban rukunin kamfanonin Aliko Dangote, ya zargi wasu jami’an gwamnati da masu zaman kansu da kokarin kawo cikas ga zuba hannun jarin matatar da ya kai dala biliyan $20.
Ya ce muddin masu amfana da harƙallar mai a ƙasar nan suka fahimci za su rasa damar su to za su yi duk mai yiwuwa wajen kawo naƙasu ga matatar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne jami’an kamfanin Dangote suka koka kan cewa kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa suna zagon ƙasa ga matatar man ta hanyar kin sayar da danyen man kan farashin da ya haura dala 4 sama da yadda aka saba.
Hakan ya sa majalisar dokoki ta umarci Kamfanin (NNPC) da ya sayar da danyen man ga Dangote a kuɗin Naira saɓanin dalar Amurka.
Ana sa ran matatar za ta samar da ganga 650,000 a kowace rana nan da ƙarshen shekara, kuma duk da haka ta fara samar da man dizal da na jiragen sama ga ‘yan kasuwa, inda ake sa ran fara samar da man fetur a cikin watan Agustan nan da muke ciki.