• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Wanda Ya Bar Gida, Gida Ya Bar Shi

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Gida

Yayin da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO), ta sanar da sanya ginin da ya raba birnin Beijing da hamadar Badain Jaran da yankin kiyaye tsuntsaye masu kaura, wanda ke kusa da gabar rawayen teku da tekun Bohai na kasar Sin, cikin jerin kayayyakin gargajiya na duniya da aka yi gado, shugaban kasar Xi Jinping, ya bukaci a kara kokarin kare al’adu da abubuwa masu daraja. 

Al’adun gargajiya su ne asali da madubin dubawa ga duk wata al’umma, kuma duk wata al’umma da ta rasa al’adunta, duk ci gaban da za ta samu, to ta rasa asalinta. Shi ya sa Hausawa kan ce, “duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi.”

  • Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam
  • Xi Ya Nanata Bukatar Kare Al’adu Da Kayayyakin Gargajiya Na Sin

A lokacin da na dauka ina zaune a kasar Sin, na lura cewa, gwamnatin da al’ummar Sinawa na daukar al’adunsu da tarihi da kayayyaki da wuraren gargajiya da muhimmancin gaske. Haka kuma, wani abu da kan burge ni shi ne, ban taba haduwa da wani Basinen da bai san asalinsa ko tarihi ko al’adun kasarsa ba.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Duk da cewa kasar Sin ta bude kofarta ga duniya, kuma ana kara samun cudanya tsakanin al’ummarta da na kasashen ketare, ko kadan bai sanya sun yi watsi da al’adunsu ko sun ari na wasu ba, har kullum, su kan yi abubuwa ne da suka dace da al’adunsu da yanayin kasarsu.

A wannan gaba da kasar Sin ta dukufa kan zamanintar da kanta, a daya bangaren, tana dukufa wajen karewa da kara yayata al’adunta, domin samun fahimta da jituwa tsakaninta da sauran al’ummomin duniya.

Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, sanya wadannan kayayyaki cikin jerin na UNESCO na da muhimmanci ga aikin zamanintar da kasar Sin. Wato yayin da ake zamanintar da kasar Sin, ba za a bar batun raya al’adun a baya ba, kuma wannan a ganina, na daya daga cikin dalilan da suka sa kasar ke samun ci gaba da zaman lafiya tsakanin al’ummominta da kuma darsuwar kishin kasa a zukatan su.( Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
Jihar Bauchi Ta Lashe Lambar Yabon Kwazo A Bangaren Mai Da Iskar Gas

Gwamnan Bauchi Ya Sassauta Dokar Hana Zirga-zirga A Katagum

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.