Shugaban kungiyar Izala na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, da ya binciki kuɗaɗen da abinci da ake bai wa gwamnonin jihohi domin raba wa talakawa.
Malamin ya bayyana haka ne, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a gidansa da ke Katsina, dangane da zanga-zangar yunwa da matsin rayuwa da matasa ke yi a Nijeriya.
- Rashin Aiki Ga Matasa Babbar Barazana Ce Ga Nijeriya – Obasanjo
- Ndume Ya Ba Ganduje Haƙuri Kan Kalaman Da Ya Yi Kan Tinubu Da Suka Yi Sanadin Sauke Shi
Malamin ya ƙara da cewa gaskiyar magana ita ce wannan taimako shugaba Tinubu yake bayarwa baya kai wa da talakawa.
Haka kuma ya yi kira ga waɗanda aka ɗora wa amanar al’umma musamman gwamnoni da su ji tsoron Allah wajen rabon tallafin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa.
“Ina kira ga ‘yan siyasa da kada su riƙa boye abincin da ake ba su, suna siyasa da shi, ina so ku sani, hatta ayyukan tituna da kuke yi idan yunwa ta kashe mutane wa za ku yi wa aikin?” in ji shi.
A cewarsa, a irin wannan yanayi da ƙasa da al’umma suka tsinci kansu, ya kamata a ɗebo kuɗi daga ko ina domin magance wannan matsala ta yunwa da matsin rayuwa da jama’a ke fama da ita.
Kazalika, ya ce duk gwamnan da aka bai wa irin wannan kuɗaɗen da kayan abinci domin a fitar da al’umma daga cikin wannan yanayi, ya ce su ji tsoron Allah su isar da wannan sako ga waɗanda abin shafa.
Da juya kan batun zanga-zanga, malamin ya ce akwai takaici irin yadda matasa suka koma barayi suna kwashe duniyoyin al’umma da sunan zanga-zanga.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar sun kama duk wanda ya taɓa kayan jama’a domin gurfanar da shi a gaban kuliya.
“Irin wannan abubuwan ne muka hango tun kafin a fara wannan zanga-zanga amma wasu suka riƙa zagin Malamai cewa an ba su kuɗi ne su hana matasa yin zanga-zanga, a zahirin gaskiya maganar ba haka ta ke ba,” a cewarsa.
Ya ƙara jaddada cewa lallai ya kamata Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohi da sake karatun ta nutsu kan batun matas, a yi sabon tunani game da makomarsu ta hanyar fitowa da sabbin tsare-tsare na gwamnatin domin koya masu sana’a da ba su jari.
Ya ce a matsayinsu na malamai duk abin da ya taso suna iya baƙin ƙoƙarinsu domin ganin an warware komai cikin maslaha.
Malamin ya ce ‘yan jaridu suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an kawo karshen wannan zanga-zanga fiye da gwamnati da kuma jami’an tsaro.
Ya ƙara da cewa idan ‘yan jaridu suka yi amfani da alƙalumansu da hikimar da Allah Ya ba su, lallai za su iya kashe wutar zanga-zangar ake yi a Nijeriya.