Ministan Kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa Nijeriya na kashe dala miliyan 600 a kowane wata wajen shigo da man fetur.
Ministan ta ce hakan na da nasaba da yadda makwabtan kasashe, har zuwa tsakiyar Afirka, ke amfani da man fetur din Nijeriya ke shigowa da shi.
- Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Jihar
- Kasar Sin Za Ta Gina Sabon Tsarin Samar Da Wutar Lantarki
Edu, ya ce hakan ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu cire tallafin man fetur don samun damar rage kashe kudi, domin ba a san adadin man da ake amfani da shi a cikin gida ba.
Tun daga lokacin da aka cire tallafin ranar 29 ga watan Mayu, 2023, shigo da man fetur zuwa Nijeriya ya ragu.
Edun ya nuna cewa duk da cewa tallafin man fetur yana taimaka wa al’umma, amma ya ce ba a yin amfani da shi yadda kamata ba.
A cewarsa kasashen ketare sun fi Nijeriya amfana da tallafin man fetur fiye da ita kanta Nijeriya.
A cewarsa Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali kan inganta yanayin tattalin arziki da kuma saukaka farashin kayan abinci.
Gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen inganta yanayin tattalin arziki da tallafa wa manoma na cikin gida yayin da ake shigo da abinci don rage hauhawar farashin kayan abinci.