Kamfanin fasaha na Kylinsoft na kasar Sin, ya fitar da manhajar na’ura mai kwakwalwa mai hade da fasahar kwaikwayon tunanin bil adama ko AI, wadda ta zama sabuwar manhajar Kylin da kamfanin ya inganta matsayinta.
Kamfanin Kylinsoft ya gabatar da manhajar ne yayin taron masu ruwa da tsaki a fannin kirar manhajojin na’ura mai kwakwalwa na shekarar bana, wanda ya gudana jiya Alhamis a nan birnin Beijing.
- Yawan Kudin Cinikin Samar Da Hidima Na Shigi Da Fici A Farkon Rabin Bana A Kasar Sin Ya Karu Da 14%
- Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa
Da wannan ci gaba, kasar Sin ta fitar da manhajar sarrafa na’ura mai kwakwalwa ta farko kirar kasar mai hade da fasahar AI, wanda hakan ya rufe gibin da kasar ke da shi a fannin samar da manhajojin na’ura mai kwakwalwa a cikin gida.
Ana fatan wannan sabuwar manhaja za ta zamo tushen samar da na’urori masu kwakwalwa, da hade matsayin manyan manhajojinsu da bangarorin cin gajiyar kwamfuta, ta fuskar tallafawa ayyukan fasahar AI, da tsarawa da aiki da su.
A baya dai kamfanonin Turai da Amurka ne ke kan gaba a duniya wajen kera manhajojin kwamfuta a duniya. Sai dai kuma da wannan ci gaba da Sin ta samu, yanzu haka ta kama hanyar shiga a dama da ita a wannan fage. Bugu da kari, saurin ci gaban kasar a fannin raya fasahar AI, na kara bude sabbin damammaki a fannin kirar manhajojin kwamfuta a kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)