Kamfanin abinci na BUA ya samu ribar kashi 38 cikin dari wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 130 a karshen watan Yuni na wannan shekarar 2024, in aka kwatanta da ribar Naira Biliyan 95.18 da ya samu a shekarar 2023, wannan na samuwa ne duk kuwu da matsalar tattalin arziki da da ake fuskanta a sassan duniya.
Wannan bayanan sun fiton e a rahoton rabin shekara da kamfanin ya fitar kwanan nan.
- Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista
- Dawo Da Tallafin Man Fetur Zai Ƙara Ta’azzara Talauci – Gwamnati
Rahoton ya kuma ci gaba da bayyana cewa, kamfanin ya samu karin kudin shiga na kashi 110 wanda ya kai naira biliyan 672.3 a shekarar 2023 kuma naira biliyan 320.9 da aka samu an samu wannan karin ne daga cinikin da aka samu na suga, fulawa da makaroni.
Rahoton ya kuma ce, wannan nasarar da aka samu ya samu ne sakamakon karin kashi 88 (Naira biliyan 369.7 daga Naira Biliyan 196.5) da aka samu a sayar da flawa da suga da makaroni.
Da yake tsokaci a kan lamarin, manajan kamfani na BUA, Ayodele Abioye, ya ce, “Wata shida na farkon wannan ya zo wa kamfanin ta hannun dama, musamman ganin dinbin ribar da aka samu.
Mun yi nasara kwarai da haske ta yadda muka samu karin daga kashi 110 zuwa naira biliyan 672.3 in aka kwatanta da abin da aka samu a shekarar 2023. Ya ce, wannan ya samu ne sakamakon goyon bayan hukumar gudanarwa da jajircewar ma’aikatanmu.