Sau da dama mu kan nakalto Pierre de Coubertin, wanda ya kafa kwamitin Olympics na kasa da kasa kuma aka fi sani da uban wasannin Olympics na zamani, inda ya ce, “Shiga gasar wasannin Olympics ya fi lashe gasar muhimmanci, saboda muhimmin abu a rayuwa ba shi ne yin nasara ba, amma yin fafutuka cike da kwarin gwiwa shi ne nasara. Yada wadannan ka’idoji na karfafa gwiwa, da jarumta, da gina bil Adama mai kishi da karimci.” Tabbas wannan batu haka yake, saboda gasar wasannin Olympics ta dade da sauya manufarta ta zakulo mafi kyawun ‘yan wasa a duniya, yanzu ta zama dandalin cudanyar bil’adama, bege da mafarkai, da zaman lafiya da hadin kai. Wasanni gaba daya, musamman wasannin Olympics, na hada kan jama’a ba tare da la’akari da bambancin matsayi na shugabanci, ko siyasa ko addini ba. Kasar Faransa ce ta karbi bakunci gasar Olympics ta bana wadda ta gudana daga ranar 25 ga Yuli zuwa ta 11 ga Agusta. ’Yan wasa sun fafata tsakaninsu cike da kauna da kishin kasashensu a zuciya yayin da suka yi cudanya da takwarorinsa cikin nishadi da annushwa.
Bana ce ta cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiya tsakanin Sin da Faransa, kuma gasar wasannin Olympic ta sake ba da damammaki ga kasashen biyu wajen karfafa dankon zumuncin dake tsakaninsu, kuma ta yin hakan, za su sa kaimi ga yin hadin gwiwa bisa la’akari da muhimmancin samun ci gaba a duniya. A kwanakin da suka biyo bayan bikin bude gasar, mun ga sakonni da dama a kafar yanar gizo daga abokai na kasar Sin wadanda suka yaba da gagarumin gudummawa da kasar Sin ta bayar ga nasarar bikin a birnin Paris.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana ruhin Olympics a yayin da ya kai ziyara kasar Faransa a watan Mayun shekarar 2024, domin halartar bikin rufe taro karo na shida na kwamitin ‘yan kasuwa na Sin da Faransa, inda ya ce, yana kallon wasannin Paris a matsayin wata dama ga kasashen biyu wajen zurfafa dangantakarsu ta tarihi, ya kuma jaddada kudurinsu na ciyar da rayuwar bil’adama gaba. Ya ce, “Gasar Olympics wata alama ce ta hadin kai, da abokantaka da kuma fahimtar juna. Bari mu dage wajen cimma burin da kasashenmu biyu suka kulla a lokacin kulla huldar diflomasiyya, mu kara dankon zumuncin gargajiya, da aiwatar da taken Olympic na ‘Mu Kara Sauri, da Girma, da Karfi da kuma Yin Hadin Gwiwa’. Mu hada hannu don bude wani sabon zamani na hadin gwiwa tsakanin Sin da Faransa da kuma rubuta sabon babi na gina al’umma mai makoma mai ma’ana ga bil’Adama.” (Mohamed Yahaya)