Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa kamfanin kera makamai na cikin gida da ke karƙasashin Ma’aikatar Tsaro na da nufin samar da makamai da harsasan da ake bukata tare da sayar da wasu.
A jawabinsa a ranar Litinin, gabanin taron bikin cika shekaru 60 da kafa ma’aikatar kera makaman, Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa, galibin kasashen Afrika a yanzu na sayen makamai daga kamfanin na DICON.
- Nazarin CGTN Ya Bayyana Yadda Wasu Mutanen Duniya Suka Soki EU Game Da Takkadamar Cinikayya Tsakaninta Da Sin
- An Samu Ƙaruwar Garkuwa Da Mutane A Nijeriya – Rahoto
Ya ce ana sayar wa kasashen ketare makaman ne karkashin dokar 2023 da ta bayar da damar habaka bangaren don samar da kudaden shiga da kuma wadata kasa da makamai.
A shekarar 1964 ne, aka samar da kamfanin na DICON da nufin samar da makaman da Nijeriya ke bukata don rage dogaro da shigo da makamai daga ketare.
Sai dai har zuwa yanzu cinikayyar makaman da Nijeriya ke yi ta ta’allaka ne, kan hada-hadar ketare musamman a halin da ake ciki na yaki da ‘yan ta’adda.
Kafin sabuwar dokar dai, DICON na da damar samar da makaman da za a iya amfani da su a cikin gida ne kadai, sai dai daga bisani an sahalewa kamfanin kera makaman da za a sayarwa kasashen makwabta don samun kudaden shiga.