Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce ma’aikatar lafiya ta Birtaniya, (NHS), za ta sha fama idan ma’aikatan lafiya ‘yan asalin Nijeriya suka bar aiki a kasar.
Pate, ya ce a duk duniya ana neman ma’aikatan lafiya na Nijeriya, kuma kashi 67 cikin dari na ma’aikatan suna aiki ne a Birtaniya.
- An Kaddamar Da Dandalin Bunkasa Noma Da Yaki Da Fatara Na Sin Da Afirka A Kenya
- Shirin Tsaftace Ruwa Na Sin Ya Lashe Lambar Karramawa Ta Kasa Da Kasa A Fannin Kirkire Kirkire
Kuma kashi 25 cikin dari na ma’aikatan lafiya na gwamnatin Birtaniya, ‘yan Nijeriya ne.
Ya kara da cewa ana son likitoci Nijeriya da ma’aikatan jinya kuma wannan abu ne da kasar za ta yi alfahari da shi.
Ministan, ya bayyana hakan ne a hirar da tashar talabijin ta Channel ta yi da shi a ranar Laraba.
Ya kuma yi magana a kan sabuwar manufar Nijeriya a kan ficewar ma’aikatan lafiya na kasar.
Ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabuwar manufar, da za ta yi maganin barin kasar da ma’aikatan lafiyar ke yi zuwa kasashen waje.