‘Yansanda a jihar Kano, sun samu nasarar ceto mutum arba’in da biyu daga hannun masu garkuwa da kuma wasu mutum ashirin da biyar daga masu safarar mutane.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Sama’ila Shu’aibu Dikko nr ya bayyana haka lokacin da suke tattauna wa da kungiyar abokan ‘yansanda da kuma wasu jami’an ‘yansanda a matsayin wata hanya ta sharer fage kafin yi ritaya daga aiki, wanda kuma za a iya cewa, a halin lokaci ya tawo.
Kamar yadda ya ce “Abin alfahari ne a gurina kasancewar ni ne kwamishinan ‘yansanda na arba’in da biyu yanzu haka ya shafe wata goma sha bakwai da kwana shida tun da ya fara aiki a jihar Kano, na fara aiki a jihar Kano a matsayin kwamishina na 42, ranar 19, watan Fabarairu 2021”.
“Da yardarm Allah zan yi ritaya daga aiki, zan yi ritaya daga aikin dansanda ranar 27 ga watan Yuli, 2022, bayan na shafe shekara sittin a duniya.”
Yay aba wa manyan jami’an ‘yansandan jihar Kano kan namijin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen aikata manyan laifuka.
Ya ce, lokacin da yake aiki, ‘yansanda sun samu nasarar kubutar da mutum dari da sittin daga wasu miyagun mutane, da wadanda aka yi garkuwa da su mutum arba’in da biyar da masu fataucin kwayoyi ashirin da biyar da nutun biyu da za yi safararsu.
Ya kara da cewa, akwai wadanda ake zargi mutum biu da Boko Haram da kuma wasu mutum uku ‘yan ta’adda sannan an kana mutum dari uku da talati da takwas da laifin fashi da makami da mutum dari da saba’in da biyu wadanda ake zarginsau da gaekuwa da mutane suki yarda suka kama wanda ake zargin.
A karshe, ya bukaci al’umma su kara hada kai domin tunkarar dukkan matsalar da ka iya taso wa.