Masu garkuwa da mutane sun sake sace matar shugaban Fulani (Ardo) na Kwali da ke Abuja, Alhaji Adamu Garba Ardo, Malama Habiba Adamu.
Matar wacce a watan Fabrairu aka yi garkuwa da ita daga baya wasu ‘yan banga suka kwato ta. An sake yin garkuwa da ita a daren ranar Litinin da ‘ya’yanta uku; Hafsat, Fatima da Abubakar.
- Da Dumi-Dumi: Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Gwamnatin Kogi
- Gwamnatin Ce Ta Harzuka Wanda Suka Sace Mu, Suka Fara Dukanmu -Wanda Ya Kubuta
An yi garkuwa da su ne kasa da awa 24 da ‘yan bindiga suka sace wasu ma’aurata, Mista Sunday Odoma Ojarume da matarsa Misis Janet Odoma Ojarume, a kauyen Sheda duka a Kwalli.
Babbar matar Ardon Fulanin, Khadijat Adamu, ce ta tabbatar wa ‘yan jarida yin garkuwa da kishiyarta a ranar Talata.
Ta ce, ‘yan bindigan sun mamayi unguwar Tudan Fulani da ke kauyen Yangoji a karamar hukumar Kwali da ke Abuja wajen karfe 12:04 na dare, inda suka kutsa cikin gidansu ta mashigar baya na dakin dafa abinci.
Ta kara da cewa, masu garkuwan sun yi yunkurin yin garkuwa da ita amma bayan da suka fahimci ba za ta iya tafiya ba sakamakon tsufanta ne suka rabu da ita.
Ta kara da cewa sun shiga cikin dakinta suka sace mata wayoyi guda uku tare da neman inda ta ajiye kudadenta.
Khadija ta ce mijin nasu baya gida a lokacin da ‘yan bindigar suka kai musu harin, ta ce ‘yan sandan caji ofis din Kwalli sun ziyarci gidan bayan da lamarin ya faru.
Kakakin ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ba ta amsa sakon karta kwana da aka tura mata kan lamarin ba.