Duba da yanayin tsadar rayuwa da al’umma ke ciki, Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta aminta da siyo shinkafar Naira biliyan 14 domin sayarwa jama’a a cikin farashi mai rahusa.
Gwamnatin ta bayyana cewar za ta siyo motar shinkafa 300 da manufar sayarwa cikin farashin mai sauki domin saukakawa al’umma tare da ragin kashi 40 zuwa 45.
- WATA SABUWA: Ganduje Ya Nuna Rashin Jin Daɗi Bayan Tinubu Ya Masa Tayin Muƙamin Jakada
- Birtaniya Za Ta Wahala Idan Likitocin Nijeriya Suka Bar Kasar – Ministan Lafiya
Kwamishinan Kananan Hukumomin jihar, Ibrahim Dadi Adare ne, ya bayyana hakan a karshen taron majalisar zartaswar gwamnatin jihar a ranar Laraba a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu.
Ya ce shirin hadin guiwa ne tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi 23.
Ya ce majalisar ta aminta da siyo shinkafar ne, duba da halin matsin da mafi yawan al’ummar Sakkwato ke ciki wanda hakan zai sa a siyo abincin tare da sayarwa cikin sauki.
A karkashin tsarin, kowace daya daga cikin mazabu 244 da ke Sakkwato, za ta samu motar shinkafa daya.
Za a raba abincin ne cikin tsarin da zai kai ga jama’a.
Za a sayar da shinkafar ne mai nauyin kilogiram 50 da kilogiram 25 da kuma kilogiram 10, daidai da karfin magidanta.