Kungiyar Kwadago ta Kasa(NLC) da sauran dukkan gwamayyar kungiyoyi da suka gudanar da zanga-zangar lumana ta kwanaki biyu a fadin kasar nan, sun bayyana cewa ba za su sarara ba har sai gwamnatin tarayya ta kawo karshen yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU).
Sun bayyana cewa manufar wannan zanga-zangar dai ita ce, tilasta wa gwamnatin tarayya ta biya bukatun ASUU, domin a bude jami’o’in gwamnatin taraya ta yadda dalibai za su ci gaba da daukan darasi.
Yadda ’Yan Kasuwa Suka Rufe Kasuwanni A Legas Don Yankar Katin Zabe
Da yake jawabi ga ma’aikata a Abuja, shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ya jaddada cewa, kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai gwamnatin tarayya ta biya dukkan bukatun kungiyar ASUU.
Kwamared Wabba ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa yaran talakawa za su ci gaba da zama a gidan iyayensu na tsawan watani biyar, yayin da ‘ya’yan masu kudi suke ci gaba da karatu a kasashen ketare.
Ya ce, “Babu adalci a cikin wannan lamari idan har gwamnati ta kasa kawo karshen lamari, ba za mu taba gajiya ba kuma ba za mu yi fushi ba, saboda ba wannan yarjejeniya muka kulla da shugabannin da muka zaba ba.
“Wannan somin-tabi ne, dole ne ku yi shirin fargfado da bangaren ilimi, mun gaji da halin ko-in-kula na gwamnati, dole ne mu rungumi kaddara a hannunmu.
“Sun ce muna janyo barazanar tsaro, amma abin da su suke yi baraza ce da dimokuradiyya, za mu sake saita kasar nan ta yadda shugabanninmu za su gudanar da abubuwan da suka dace.
“Muna yaba wa gwamnoni wadanda suka fito domin yin jawabi, muna bukatar gudanar da tattauna ta yadda za a kawo karshen lamarin, ba za mu taba yarda mutane kalilan su ruguza goben yaran Nijeriya ba,” in ji shi.
Shi ma da yake gabatar da jawabi, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa dole ne gwamnatin tayya ta kaddamar da tsarin gudanarwa na biyan malaman jami’o’i.
Hakazalika, kungiyar NLC reshan Jihar Legas ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makanni biyu na kawo karshen yajin aikin ASUU ko kuma ta fuskanci zazzafar zanga-zanga.
Shugaban kungiyar NLC reshan Jihar Legas, Kwamared Agnes Funmi Sessi shi ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a gaban dinbin masu zanga-zanga a ofishin gwamnatin Jihar Legas. Ya nuna takaicinsa ta yadda iyaye da dalibain jami’o’in gwamnatin tarayya suke ciki, inda ya ce shi ne makasudin gudanar da wannan zanga-zanga na gargadi.
A ranar 26 ga watan Yulin 2022, kungiyar NLC ta gudanar da zanga-zangar gargadi na kwanaki biyu a dukkan fadin kasar nan, sakamakon gwamnatin tarayya ta kasa kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU. Kungiyar ta gargadin gwamnatin tarayya kar ta dauki wannan zanga-zanga da wasa, domin idan har ta yi kunnen kashi, to zanga-zangan za ta iya rikidewa fiye da wanda aka samu na EndSARS a shekarar 2020.
Kungiyar ASUU ta tsunduma cikin yajin aiki na tsawan watanni biyar, sakamakon rashin cika mata alkawarin da gwamnatin tarayya ba ta yi ba, wadanda suka hada da alawus din malaman jami’o’i da gyara tsarin jami’o’in Nijeriya.