Ba da jimawa ba da rufe gasar wasannin Olympics na Paris, sai kafofin yada labarai na kasar Amurka suka bayyana damuwarsu cewa, “Ya zuwa shekarar 2050, akasarin sassan duniya ba za su iya gudanar da wasannin Olympics ba sabo da tsananin zafi”. A hakika, duniya na ta kara zafi, kuma bil Adama na kara fuskantar matsanancin yanayi irinsu fari, da ambaliya da sauransu. Mai yiwuwa a nan gaba, za a iya gudanar da wasannin Olympics na lokacin zafi ne kawai a kudancin duniyarmu a lokacin da suke dari.
Domin tinkarar matsalar sauyin yanayi, a shekarar 2020 kasar Sin ta sanar da burin da take neman cimmawa, na kaiwa kololuwar fitar da hayakin Carbon mai dumama yanayi kafin shekarar 2030, da kuma daidaita hayakin Carbon da abubuwan da za su zuke shi kafin shekarar 2060. Yanzu shekaru hudu ke nan, kuma ga shi kasar Sin ta cimma nasarorin a zo a gani a wannan fanni, kuma alkaluman da aka fitar sun shaida cewa, fadin dazuzzukan da aka dasa a kasar Sin ya kasance na farko a duniya, kuma kasar ita ce kasar da dazuzzukanta suka fi saurin karuwa a duniya, karuwar da ta kai kimanin kaso 1/4 na duk duniya cikin shekaru kusan 20 da suka wuce. Baya ga haka, Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi saurin rage yawan makamashin da suke amfani da shi wajen samar da kayayyaki, kuma ta fi saurin raya makamashin da ake iya sabuntawa a duniya, kana yawan makamashi da ake iya sabuntawa da kasar Sin din ke samarwa na kan gaba a duniya, kuma kasar ta kafa cikakken tsarin samar da sabbin makamashi mafi girma a duniya.
- Ɗan Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma Zai Biya Naira Miliyan 10 A Kano
- Sin Na Shirin Amfani Da Fasahohin Dijital Wajen Bunkasa Magungunan Gargajiya Na Kasar
Ban da haka, a gun wani muhimmin taron da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mai mulki a kasar, ta kira a kwanan baya, jam’iyyar ta sanar da jerin abubuwan da taken neman cimmawa ta fannin kara zurfafa yin gyare-gyare, ciki har da “gaggauta sauya salon bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma ta yadda zai zama mai kiyaye muhalli daga dukkan fannoni”. A kwanakin baya kuma, kwamitin kolin jam’iyyar da kuma majalisar gudanarwar kasar sun samar da “ra’ayoyi a kan gaggauta sauya salon bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma ta yadda zai zama mai kiyaye muhalli daga dukkan fannoni”, kuma hakan ya zama karon farko da kasar Sin ta tsara ayyukan da suka shafi gaggauta sauya salon bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma ta yadda zai zama mai kiyaye muhalli daga matakin kasa.
Duk wadannan abubuwa sun faru ne sakamakon niyyar kasar Sin ta aiwatar da tunanin nan na “kyakkyawan muhalli kadara ce mai kima”. A sakamakon wannan tunani, duniya ta shaida yadda kasar Sin ta yi ta kara kyautata, haka kuma ya haskaka wa kasashe masu tasowa hanyar tabbatar da dauwamammen ci gaba.
Hasali ma dai, kasar Sin ta riga ta aiwatar da daruruwan shirye-shirye masu nasaba da samar da makamashi masu tsabta, da kuma tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, kuma yawan lantarki da tashoshin samar da wutar lantarki ta zafin rana da kamfanonin kasar Sin suka gina tare da hadin gwiwar kasashen Afirka suke iya samarwa, tuni ya zarce KW miliyan 1.5, matakin da ya sa kasar ke sahun gaba a duniya wajen aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ta fannin kiyaye muhalli.
Yau rana ce ta kiyaye muhalli ta kasar Sin a karo na biyu. Duniyarmu gida ne na bai daya ga dukkanin dan Adam, kuma makomar dan Adam daya ce a fannin tinkarar matsalolin muhalli. A yayin da kasar Sin ke ci gaba da kokarin inganta muhallin halittu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da samar da gudummawa, da hada hannu da sassan kasa da kasa, musamman ma kasashen Afirka, don kara inganta muhallin duniyarmu baki daya.