Jihohin Nijeriya sun kashe naira biliyan 139.92 daga cikin kudaden da suka karba a wurin gwamnatin tarayya a watanni 6 na farkon shekarar 2024.
Wannan bayanai dai yana kunshe a cikin kididdigan da kwamitin asusun rarraba kudade ta tarayya wacce ta samu daga bayanan hukumuar kididdiga ta kasa (NBS).
Kudaden da aka kashe ya kkaru da kashi 122% daga naira biliyan 63.06 da aka kashe a shekarar da ta gabata na watanni shidar farkon shekara.
- Yadda Mutane Ke Tona Ramin Tururuwa Don Neman Abinci A Borno
- An Yi Watsi Da Ayyuka Na Fiye Da Naira Tiriliyan 17 A Nijeriya – Cibiyar CIPMN
Bayanan ya nuna cewa jihohin sun kashe naira biliyan 9 zuwa naira biliyan 20 a kowacce wata, wanda ya ninka bashin da ake bi sakamakon faduwar darajar naira.
A watan Janairun 2024, jihohin Nijeriya sun kashe naira biliyan 9.88 wajen biyan basussuka a waje, wanda ya ragu daga naira biliyan 13.7 a watan Janairun 2023. A nan an sami ragowar kashi 27.7%, wanda yake nuna cewa wasu jihohi ba su da basussukan sosai.
Haka kuma canjin dala na tsakanin naira 830 zuwa 1,000 wanda shi ne mafi kankanta a wannan rahoton.
A watan Fabrarun 2024 kuwa, an biya bashin naira biliyan 24.53, wanda aka sami karin kashi 148%, inda ya karu daga naira biliyan 9.88 na watan Fabrarun 2023.
A watan Maris 2024, an biya bashin naira biliyan 40.41, wanda hakan ke alamta cewa an sami karin kashe 309%, idan aka kwatanta da watan Maris ta 2023 da aka biya naira bilyan 9.88.
Daga watan Afrilu zuwa Yuni shekara ta 2024, jimillar bashin da aka biya shi ne, naira biliyan 21.70 a kowacce wata idan aka kwatanta da naira biliyan 9.88 da aka biya na shekarar 2023, kudin da aka kashe ya karu da kashi 119.70% a kowacce wata.
Jihohin Kaduna da Lagos su ne suka fio biyan bashi a kan kowacce jiha, don bashin da jihohin suka biya ya karu daga naira biliyan 16.88 a watannin shida na farkon shekarar 2023, inda a yanzu ya koma naira biliyan 32.44 a wannan shekarar ta 2024, Kenan an sami karin kashi 92%, wadannan jihohin guda biyu sun kashi 40% na bashin da ake binsu.
Haka kuma jihohin Kuros Ribas da Bauchi sun sami karin bashin da ake binsu. Inda Kuros Ribas ta biya Naira biliyan 2.21 a shekarar 2023 a wannan shekarar kuwa ya koma naira biliyan 7.87, an sami karin kashi 256%. A yayin da Jihar Bauchi a shekarar 2023 sun biya naira biliyan 3.28 a wannan shekarar kuwa sun biya naira biliyan 6.33 hakan na nuna cewa an sami karin kashi 93%.
Jihar Ogun sun sami karin biyan bashi a kasashen waje daga naira biliyan 1.57 a shekarar 2023 zuwa naira biliyan 4.29 a shekarar 2024, wanda aka sami karin kashi 173%, haka lamarin yake a Jihar Oyo inda abun ya karu daga naira biliyan 2.61 a shekarar 2023, ya koma naira biliyan 6.36 a shekarar 2024 wanda ke nuna an sami karin kashi 144%.
Jihar Ribas ma haka take don an sami karuwar bashi a kasashen waje daga naira biliyan 1.76 da aka biya a watannin shidar farkon shekara ta 2023 zuwa naira biliyan 4.62 a watanni shidar farkon shekara ta 2024, wanda ke nuna cewa an sami karin kashi 162% idan aka kwatanta shekarun.
Wadannan bayanan sun kara nuna yadda kudaden da Nijeriya ke samu suke karewa wajen biyan basussuka a waje.