Da karfe 4 saura mintuna 25 na yammacin Juma’ar nan bisa agogon birnin Beijing ne kasar Sin ta yi nasarar harba gungun taurarin dan adam, na binciken doron kasa ta amfani da rokar Long March-4B, daga tashar harba kumbuna ta Xichang, dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
Bayan harba su, taurarin dan adam din rukunin Yaogan-43 01, sun shiga falakin su kamar yadda aka tsara. Ana kuma sa ran amfani da su wajen gudanar da gwaje gwaje kan sabbin fasahohi, na nazarin sassan falaki mara nisa daga doron duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)