A yau Asabar ne ake sa ran shugabannin kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ko SADC, za su hallara a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe, domin gudanar da taron shekara shekara karo na 44.
Shugabannin za su gudanar da taron ne a sabon ginin zauren ‘yan majalissun dokokin Zimbabwe, wanda kasar Sin ta tallafa wajen ginawa, wanda kuma ke kan shahararren tsaunin nan na Hampden, mai nisan kilomita 18 daga birnin Harare.
- Dakatar Da Harajin Shigowa Da Abinci: Gwamnati Za Ta Yi Asarar Kudin Shiga Naira Biliyan 188.37
- Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano
Harabar ginin dai na da fadin sakawaya mita 33,000, yana kuma da manyan sassa 2, sassan ofisoshi mai hawa 6, da ginin zaurukan ‘yan majalissa mai hawa 4.
A watan Oktoban bara ne gwamnatin kasar Sin ta mika sabon ginin ga gwamnatin Zimbabwe a hukumance. Kuma taron shekara shekara na kungiyar SADC da za a bude a yau, shi ne babban taro na farko da gwamnatin kasar za ta karbi bakunci a sabon ginin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)