Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta bayyana cewa sakamakon dakatar da harajin shigo da kayayyakin abinci da Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi, zai janyo gwamnatin tarayya ta tafka asarar kudaden shiga har naira biliyan 188.37 na tsawon watanni shida na aiwatar da umarnin shugaban kasa.
A watan Yulin bana ne dai Shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da harajin shigo da kayan masarufi a matsayin wani bangare na dabarun rage farashin kayan abinci da kuma dakile yunwar da ake fama da ita a fadin Nijeriya.
- Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Na Duniya Da Rahoto Gaskiya Kan Nijeriya
- Dalilan Da Suka Sabbaba Karancin Abinci A Nijeriya — Masana
Shugaban kasa ya ce gwamnati ta dauki wannan na yin asarar kudaden shigar ne domin tabbatar da wadatar abinci da daidaita farashi a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, wanda ya bayyana yadda tsarin ya shafi kudaden shiga a ranar Talata, ya kuma ce yanzu haka hukumarsatana jiran kaddamar da ka’idojin da ma’aikatar kudi ta tarayya kafin a aiwatar da tsarin.
Adeniyi ya bayyana hakan ne a wajen lacca na kaddamar da littafi don karrama shi mai taken, “Tasirin Hulda da Jama’a Ga Mahukuntan Hukumar Kwastam”.
Shugaban Kwastam ya ce gwamnati ta samu naira tiriliyan 3.819 a matsayin kudaden shiga daga abubuwan da abin ya shafa a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023. “Mun himmatu wajen aiwatar da umarnin shugaban kasa,” in ji Shugaban Hukumar Kwastam.
Ya yi alkawarin tura jami’ai na musamman da aka horar don aiwatar da tsarin tare da samar da sakamako mai kyau da suka yi daidai da manufar shugaban kasa.