Tun bayan da kungiyar ta tabbatar da sabon kociyan, tuni masu sharhi a kan kwallon kafa a Nijeriya suka fara tattaunawa a kan ko sabon mai koyarwar zai kai kungiyar ga nasara bayan koma baya da aka samu a ‘yan shekarun nan.
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta gabatar da sabon kociyanta, Usman Abdallah a farkon wannan watan, wanda zai ja ragamar kungiyar kan yarjejeniyar kakar wasa guda biyu da cewar za a tsawaita masa wata 12 idan ya taka rawar gani.
- Jan Aikin Da Ke Gaban Sababbin Shugabannin Kano Pillars
- Dalilan Amai Da Gudawa Na Yara Lokacin Fitar Hakori
Kano Pillars ce kan gaba a yawan magoya baya a fadin kasar nan, magoya baya na hakika da suke cika filin wasa na Sani Abacha, duk ranar da take buga wasa a gida haka kuma dubban magoya bayanta kan bi kungiyar wasannin da take yi a waje da ya hada da na Premier ko na kalubalen kasar, saboda kishin da suke yi wa kungiyar.
Kano Pillars ta lashe kofin Premier na Nijeriya hudu da na kalubale biyu, wadda sannan ta wakilci Nijeriya a gasar cin kofin Afirka na ‘Champions League’ da ‘Confederation Cup’ a shekarun baya, lokacin da kungiyar take kan ganiyarta. Kungiyar kan taka rawar gani a gasar Premier ta Nijeriya, musamman karawa da Enyimba da Rangers da National da babban wasan hamayya tsakanin kungiyar da kuma kungiyar Katsina United da dai sauransu.
To sai dai kungiyar ta ci karo da koma baya, wadda rabon da ta dauki kofin Premier tun 2014, amma ta lashe FA Cup a 2019, wadda rabon da wata kungiya a Kano ta lashe shi tun 1953, sannan kuma rabon da kungiyar ta buga gasar Afirka tun 2020, wadda aka yi waje da ita a zagayen neman shiga wasannin, wanda aka fi sani da ‘Play-Off’.
Kungiyar Kano Pillars ta ci karo da matsaloli da yawa da ya kassara kwazon kungiyar tun daga rashin bayar da kudi a lokacin da ya dace daga gwamnati, sannan wasu matsalolin ana danganta su da rashin daukar ‘yan wasan da suka dace da rashin kwazon ‘yan wasa da yawan tarzoma daga magoya a gida da dai sauransu.
A kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 aka ci tarar Kano Pillars Naira miliyan bakwai da dubu dari biyar, bayan da aka samu kungiyar da karya dokar hukumar gasar kasar da ta NFF. Dokar ta kunshi hana nuna wasa kai tsaye a talabijin da tayar da hatsaniya daga ‘yan kallo a karawa tsakanin Akwa United da Kano Pillars.
Pillars ta fadi daga gasar Premier ta kasa ranar 16 ga watan Yulin 2022, bayan matsalolin da suka baibaye ta kuma kungiyar ta fuskanci hukuncin masu gudanar da gasar Premier ta Nijeriya, bayan da aka samu shugabanta Surajo Janbul a karawa da Dakkada.
A 2019 Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da nada Surajo Sha’aibu Yahaya da ake kira Jambul, wanda ya maye gurbin Alhaji Tukur Babangida, sai dai Jambul ya karbi ragama lokacin da Pillars ke dab da lashe ‘Federation Cup.” da kuma ta biyu a babbar gasa ta kasa.
To sai dai a kakar aka yi waje da Pillars a CAF Champions League a wasannin cike gurbi, inda Asante Kotoko ta Ghana ta ci 5-2 gida da waje, haka kuma a kakar gaba aka yi waje da Pillars dagga CAF Confederation Cup, inda wata karamar kungiya daga Senegal ta yi nasara 3-1 gida da waje.
Sakamakon hatsaniyar da magoya bayan Pillers ke yi a yayin da kungiyar take wasa ya sa kungiyar aka dauke ta daga buga wasannin ta na gida a filin was ana Sani Abacha, hakan ya sa ta je filaye daban-daban har guda hudu waje.
Da farko an mayar da Kano Pillar buga buga wasannin gida a filin wasana Ahmadu Bello dake Kaduna, daga nan ta koma filin Muhammadu Dikko a Katsina, sannan a Katsina ma an samu hatsaniya, inda aka mayar da kungiyar buga wasanninta Babban Birnin Tarayya Abuja, kafin daga baya ta koma gida filin wasa na Sani Abacha.
Bayan da Pillars ta dawo gida sai ta tsinci kanta a kasan teburi daga nan aka fara cuku-cukun yadda kungiyar za ta ci gaba da zama a Premier League inda daga nan ne kuma hankalin magoya baya ya tashi kan yadda Pillars ta tsinci kanta a halin kaka-ni-ka yi, wadanda suka zargi shugabanta da rashin kwarewa.
Matsin da Jambul ya fuskanta daga wajen magoya baya ya sa ya dauki doka a hannunsa, lokacin da kungiyar ke barar da maki a gida domin lokacin da Pillars ke buga mako na 31 da Dakkada a gida, kuma masu gida na cin kwallo daya, sai Dakkada ta farke dab da za a tashi daga wasan. Daga nan ne Jambul ya shiga fili da cin zarafin mataimakin alkalin wasa da bukatar a soke kwallon da aka ci Pillars, sai dai hakan ya harzuka masu gudanar da Premier, wadanda suka kori Jambul daga baya suka ce za su dauki matakin sha’ria a kansa.
Pillars ta karkare a mataki na 19 da maki 45 a kakar, bayan da ta ci wasa tara da canjaras tara aka doke ta karawa 20.Haka kuma an zura kwallo 50 a ragar Pillars, ita kuma ta ci 26 a kakar bana da hakan ya sa ta yi ban kwana da babbar gasa ta Nijeriya da aka karkare.
Dawo Da Ibrahim Galadima
Bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta sallami Surajo Shu’aibu Yahaya, sai ta nada Alhaji Ibrahim Galadima a matakin rikon kwarya inda daga nan ne Pillars ta nada Babangida Little a matakin sabon shugaban kungiyar, wanda hakan ba ta canja zani ba, kan kalubalen da kungiyar ke fuskanta.
Domin shima ya yi fama da na sa matsalolin da yawa, har da daukar sabon koci Offor Paul, wanda ya yi kwana 19 aka maye gurbinsa da Usman Abdallah sai dai kafin nan kungiyar ta sallami Audu Mai Kaba kafin kammala kakar bara, bayan da ta dakatar da shi ta kuma nada Ahmed Garba Yaro-Yaro a matakin rikon kwarya.
Kano Pillars ta kare a mataki na 11 a kakar da ta wuce bayan wasanni 38, wadda ba ta samu gurbin wakiltar Nijeriya ba a gasar Afiirka a bana, kuma Pillars za ta fara buga Premier ta Nijeriya ta bana da Ikorodu a Sani Abacha a kakar 2024 zuwa 2025.
Wane ne Usman Abdalla, sabon kociyan Kano Pillars
Sunan mai mkoyarwa Usman Abdalla ba boyayyen suna bane a tarihin kwallon kafa a Nijeriya, kuma ya buga wasa a gida da kuma Afirka kafin Turai, wanda ya fara daga Sanka Bipers ta Kano, sannan ya yi UNTL ta Kaduna da Rocks ta Kaduna da Stationery Stores ta Lagas da kuma Mogas 90 ta Jamhuriyar Benin.
Sannan ya buga wasa a Kano State Academic da wakilatar Jihar Kano a wasannin kasa da ake kira Festibal a shekarar 1980 da wakiltar Nijeriya ta matasa ‘‘yan kasa da shekara 20 zuwa 23 tare da dan uwansa Hassan Abdallah.
Sai dai a 1991 ya koma buga wasa a kungiyar Al Arabic da kuma kungiyar Bayer Leberkusen, ya kuma je Singapore, inda ya buga wasa a Jurong FC da Khalsa FC da kuma Gombak United FC kafin ya yi ritaya daga buga wasa a shekarar 2006. Usman Abdalla ya fara aikin horar da kwallon kafa a kasar Faransa da EPS FC da FC Sete da FC Frontignan da kuma Bollene FC, bayan da ya mallaki lasisin horarwa daga Turai a Ingila, sannan ya kuma halarci sanin makamar aikin kociyan kungiyoyin Afirka da hukumar kwallon kafar Afirka.
A Nijeriya ya koyar da kungiyar Enyimba da lashe kofin Premier Nijeriya a kungiyar da taka rawar gani a gasar Afirka ta Champions League, sai dai kafin ya karbi aikin kociyan Enyimba ya yi mataimaki a Pillars da jan ragamar karamar kungiyar.
Da farko ya je Enyimba a matakin mataimakin Paul Aigbogun daga baya aka bashi ragamar jan kungiyar, wanda ya kai dab da karshe a gasar cin kofin Zakarun Afirka wato ‘Champions League’, haka kuma ya horar da Wikki Tourist ta Garin Bauchi da Katsina United daga nan ya je hutu, inda yanzu kuma ya dawo Kano Pillars a karo na biyu, amma wannan dawowar ba a matsayin mataimaki ba, a matsayin mai koyarwa wanda kuma ake ganin kwarewarsa da ilimin sanin kwallo zai taimakawa kungiyar a kakar wasan da za a fara a nan gaba kadan.