• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
1 year ago
in Labarai
0
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi ya bukaci taimakon Gwamnatin Jihar Sakkwato, domin kubutar da shi daga hannunsu. 

‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da tsohon Sarkin Daular Gobir da ke Sabon- Birni tare da dansa kusan makonni uku a kwanar Maharba da ke a Goronyo a kan hanyarsa ta komawa gida Sabon- Birni daga Sakkwato, inda suka rika harbi ba kakkautawa wanda ya tilastawa motarsa tsayawa.

  • Hadin Gasasshen Burodi Da Kwai Da Madara
  • Shugabannin SADC Za Su Hallara A Sabon Ginin Ofishin Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa Domin Gudanar Da Taron Shekara

‘Yan ta’adda na cin karensu ba babbaka a Gabascin Sakkwato da ke da kananan hukumomi shida, inda suke kisan gilla, garkuwa da mutane, satar shanu, mayar da garuruwa kufai da tilastawa al’umma kaurace wa gona.

Da farko ‘yan ta’addan sun bukaci a biya kudin fansar Sarkin Naira biliyan daya, amma daga baya suka rage kudin zuwa Naira miliyan 500.

A wani faifan bidiyon na minti daya da ‘yan ta’addan suka saki a ranar Asabar wanda aka dauka a ranar Laraba, an nuno Sarkin cikin daji a cikin mummunan yanayi da zubar jini a rigarsa yana cewar yana jin jiki kuma gwamnatin Sakkwato ba ta taimake shi ba.

Labarai Masu Nasaba

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

“Ina rokon ‘yan uwana da masoyana da abokaina da shugabanni na cewar an kai rana ta karshe yau Laraba, don haka ina so su taimake ni. Ina sanar da su cewar wallahi, wallahi mutanen nan sun ma gaji da mu don duk abin da ake yi sun yi amma gwamnatinmu ba ta taimake ni ba, kuma ina ganin duk halin dana shiga a duniya za ta taimake ni amma ba ta taimake ni ba.”

“Ni ma’aikacin gwamnati ne shekara da shekaru ina bauta mata, na yi shekaru 45 ina bautawa gwamnati kuma duk a aikin sarauta.” cewar Sarkin wanda ba a nuno fuskar ‘yan bindigar da ke yi masa bidiyo da tambayoyi ba.

Sarkin na Gatawa ya rasa rawaninsa na babbar sarautar Sarkin Gobir na Sabon- Birni wadda ke da dadadden tarihi a watan Afrilu a yayin da gwamnatin Sakkwato ta tube rawanin Sarakuna 15 tare da sauyawa wasu masarautu.

An rage masa girma tare da mayar da shi Sarkin Gatawa, masarautar da ke karkashin ikonsa

Jim kadan da garkuwa da Sarkin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewar suna kan gudanar da bincike kan lamarin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: GarkuwaSakkwatoSarkiYan bindiga
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hadin Gasasshen Burodi Da Kwai Da Madara

Next Post

PDP Ta Lashe Zaɓen Shugabanin Ƙananan Hukumomin Bauchi Gaba Ɗaya

Related

Labarai

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

9 hours ago
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

10 hours ago
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC
Labarai

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

13 hours ago
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

16 hours ago
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
Labarai

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

18 hours ago
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

20 hours ago
Next Post
PDP Ta Lashe Zaɓen Shugabanin Ƙananan Hukumomin Bauchi Gaba Ɗaya

PDP Ta Lashe Zaɓen Shugabanin Ƙananan Hukumomin Bauchi Gaba Ɗaya

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

August 25, 2025

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.