Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta tabbatar da kashe wani hadimi ga gwamnan jihar, Sanusi Gyaza, da ɗaya daga cikin matansa a gidansa da ke unguwar Gyaza, na ƙaramar hukumar Kankia, a ranar Juma’a, inda suka yi awon gaba da matarsa ta biyu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Sadiq ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce, suna kan ci gaba da bincike kan lamarin.
- NDLEA Ta Cafke Wani Ɗan Kasuwa Ya Haɗiye Hodar Iblis Ƙulli 88 A Abuja
- Batun ‘Yan Mata Masu Yanga Wajen Tsallaka Titi
Mummunan lamarin wanda ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da jimami, ya bayyana damuwa game da yadda matsalar tsaro ke ƙara tabarbarewa a jihar, inda ayyukan ’yan daba da suka haɗa da garkuwa da mutane da kashe-kashe ke karuwa.
Ko da aka tuntuɓi babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Maiwada Danmallam, bai amsa sakon da aka aika zuwa lambar wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.