Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 tare da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin mataimakinsa.
Wannan jita-jitar ta taso ne bayan wasu fastotin Ganduje da Uzodimma da suka bayyana na takara a yanar gizo, ɗauke da taken, “Don ‘Yan Nijeriya, ci gaban arziki da haɓakar ɗan Adam.” Hotunan sun yi nuni da cewa za su tsaya takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
- WATA SABUWA: Ganduje Ya Nuna Rashin Jin Daɗi Bayan Tinubu Ya Masa Tayin Muƙamin Jakada
- Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano
Sai dai, a wata sanarwa da Edwin Olofu, Babban Sakataren yaɗa labarai na Shugaban APC na ƙasa ya fitar yau Lahadi, ya bayyana wannan zargi a matsayin ƙarya da sharri.
Ya danganta jita-jitar da wasu masu son tada zaune tsaye, musamman daga ƙungiyar Kwankwasiyya, waɗanda ke ƙoƙarin haifar da rikici tsakanin Ganduje da Shugaba Bola Tinubu.
Sanarwar ta jaddada cewa Ganduje na nan daram yana biyayya ga Shugaba Tinubu kuma ya duƙufa wajen goyon bayan shirye-shiryensa don samar da ci gaba da haɗin kan ƙasa.
APC ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da wannan shiryayyar ƙarya tare da guje wa yaɗa labarai marasa tushe.