Jam’iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta jajanta wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a fadin jihar.
A cikin wata sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun sakataren Jam’iyyar, Hon. Abubakar Bawa Kalgo, shugaban jam’iyyar na jihar, Alh Usman Bello Suru, ya bayyana aukuwar ambaliyar a matsayin “Ikon Allah”, ya kuma yi kira da a yi addu’a don rage raɗaɗin waɗanda abin ya shafa.
- An Yi Garkuwa Da Sarkin Gobir Da Wasu Mutane 5 A Sokoto
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Jam’iyyar ta kuma buƙaci hukumomin bayar da agajin gaggawa a Jihar da na ƙasa da su gaggauta ɗaukar matakai domin rage wa waɗanda lamarin ya shafa wahala.
Alh Usman Bello ya bayyana rashin jinda ɗinsa ga hukumomin gwamnatin jihar da ke da ruwa da tsaki wajen daƙile matsalar sauyin yanayi da rashin ɗaukar matakan da suka dace na rage raɗaɗin barna, duk kuwa da hasashen da hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasa (NIMET) ta yi a baya na samun ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kebbi kimanin watanni uku da suka gabata.
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa tuni wasu daga cikin zaɓaɓɓun wakilanta suka fara bayar da tallafi ga al’ummomin da abin ya shafa, yayin da wasu kuma nan ba da jimawa ba za su raba kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa a mazaɓunsu.