A gun taron manema labarai da kwamitin kula da wasannin Olympics na lokacin zafi na birnin Los Angeles ya kira a kwanan baya, ‘yan jaridar kasashe da dama sun yi tambayoyin da suka shafi batun siyasantar da wasanni, da batun bindiga da ma tsaro da sauransu, kuma damuwar da ‘yan jaridar suka nuna a tambayoyinsu ta shaida yadda kasar Amurka ta dade tana dakile abokan takararta ta hanyoyin da ba su dace ba, da ma yadda take kokarin fadada nuna fin karfi har zuwa fagen wasanni.
Gasar wasannin Olympics karo na 33 da aka kammala ba da jimawa ba a birnin Paris, ta sake shaida yadda Amurka ta yi ta siyasantar da harkar wasanni. Tun wasu watanni kafin a fara gasar, wasu hukumomi da ma kafofin yada labarai na kasar suka yi ta samar da rahotannin wai ‘yan wasan ninkaya na kasar Sin sun sha maganin kara kuzari, ba tare da yin la’akari da sakamakon bincike mai adalci da kungiyar kula da wasannin ninkaya ta duniya da hukumar yaki da shan maganin kara kuzari ta duniya(WADA) suka samar ba, sai kuma bayan da aka fara gasar, suka yi ta shafa bakin fenti ga ‘yan wasan kasar Sin da suka ci nasara. Baya ga haka, wasu ‘yan majalisun dokoki na kasar Amurka sun kuma gabatar da shirin doka ta wai “farfado da imani ga hukumar yaki da shan maganin kara kuzari ta duniya”, inda suka yi barazanar daina samar da kudin tallafi na sama da dala miliyan uku da ya kamata gwamnatin kasar Amurka ta biya hukumar a kowace shekara.
A sa’in da Amurka ke yada karairayi na zargin ‘yan wasa na wasu kasashe da shan maganin kara kuzari, a sa’i daya kuma, sun ba da kariya ga ‘yan wasansu da gwajin da aka yi musu ya shaida cewa sun sha sinadaran kara kuzari. Sanarwar da hukumar WADA ta bayar a kwanan baya ta nuna cewa, hukumar yaki da shan maganin kara kuzari ta kasar Amurka ta shafe shekaru da dama tana amincewa da ‘yan wasa da suka sha maganin su halarci wasannin.
Har kullum Amurka tana kallon kanta a matsayin kasar da ta fi karfi a fannin wasanni, wadda kuma take daukar wasanni a matsayin wani muhimmin bangare na karfinta. Sai dai yayin da kasar Sin da sauran kasashe suka yi ta samun ci gaba a fannin wasanni a cikin ‘yan shekarun baya, har suka zarce Amurka a wasu wasannin da a baya Amurka ta yi fice, misali wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ninkaya da sauransu, lamarin ya kara sa Amurka damuwa. Don haka, ta kwaikwayi matakan da ta saba na dakile kasar Sin a fannonin siyasa da tattalin arziki, ta yi ta yada karairayi don shafa wa kasar Sin da ‘yan wasanta kashin kaza, don karfafa matsayinta a fannin.
“Karin sauri da karin girma da karin karfi, da kuma karin hadin kai” shi ne taken wasannin Olympics. Takara da juna ba shi ne jigo daya kacal na wasannin Olympics ba, a maimakon haka, wasannin Olympics sun fi shafar “hadin kai da zumunta”, da ma burin da ‘yan Adam ke neman cimmawa na zaman lafiya da hadin kai da ci gaba.
A gasar wasannin Olympics na Paris, yadda ‘yar wasan Badminton ta kasar Sin malama He Bingjiao ta dauki bajin kwamitin wasannin Olympics na kasar Spaniya a lokacin da aka mika mata lambar yabo, don isar da gaisuwa da fatan alheri ga abokiyar takararta Carolina Marín Martin ‘yar kasar Spaniya, wadda ta janye jiki daga gasar sabo da raunukan da ta ji, da ma yadda ‘yan wasannin kwallon tebur na kasashen Sin da Koriya ta arewa da Koriya ta kudu suka dauki hoto tare a lokacin da aka mika musu lambobin yabo, da dai sauransu, duk sun bayyana wa duniya abun da ake nufi da wasannin Olympics.
Nan da shekaru hudu masu zuwa, za a gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin zafi karo na 34 a birnin Los Angeles na kasar Amurka, kuma daina siyasantar da wasanni ita ce bukata da buri na bai daya na kasashen duniya game da gasar. Muna fatan kwamitin kula da wasannin Olympics na Los Angeles za su samar wa ‘yan wasa wani dandali mai adalci da hadin kai da zumunci, don ‘yan wasa na kasa da kasa su nuna kwarewarsu, kuma kasashen da ke fama da baraka da rikice-rikice su sake hada kansu karkashin ruhin wasannin Olympics. (Mai zane:Mustapha Bulama)