Shugabar Gidauniyar Yaki da Sha tare da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Tsakanin Matasa ta Kasa (YADAF), Hajiya Fatima Bature Jikan Dan’uwa ta bayyana cewa dole a hada kai domin yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasan, ta hanyar fadakar da al’umma a kan barnar da shaye-shayen miyagun kwayoyi ke yi ga rayuwar al’umma musamman matasa.
Shugabar YADAF ta bayyana haka a lokacin da take fadakar da matasa illar ta’ammali da miyagun kwayoyi a ofishinta da ke Jihar Kano.
Hajiya Fatima ta ce abin takaici shi ne yadda gangamin na wannan shekarar yana zuwa ne a daidai lokacin da mu’amala da miyagun kwayoyi a tsakanin matasan ke kara karuwa a kullum. Ta ce kidididgar da aka yi a shekarar 2019, ta nuna cewa an fi shan tabar wiwi a tsakanin matasan, inda aka gano cewa akalla ‘yan Nijeriya fiye da miliyan 10.6 ke shan tabar wiwi, yayin da wasu na fara shan tabar ne tun suna shekara 19 a duniya.
Shugabar YADAF ta yi tsokaci kan binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar, wanda ya tabbatar da cewa tabar wiwi ce aka fi sha a yankin Afirka, inda aka samu kashi 5.2 zuwa 13.5 na masu shan tabar a yankin Afirka mafi yawansu kuma na yankin Afirka ta Yanma ne, ana kuma iya cewa al’amarin kwayoyin ya yi kamari a Nijeriya fiye da wata kasa a Afirka.