Barkanmu da sake saduwa a filin Ra’ayi Riga, wannan mako mun kawo muku Ra’ayoyinku ne a kan Bidiyon nan na fasinjojin da ‘yan ta’adda suka sace a jirgin kasan nan da ya fito daga Abuja zuwa Kaduna, inda ake azabtar da su.
Wani matakin gaggawa kuke ganin yakamata gwamnati ta dauka don ceto su?
Ummu Maimuna Yumnah
Gwamnati dai ta nuna gazawarta, sai muci gaba da addu’ar Allah ya kubutar da duk wani wanda yake hannusu cikin aminci, mu kuma Allah ya karemu fadawa hannun wadannan azzaluman da ba su san Allah ba.
Lami S Mudu
Ina addu’ar Allah ya fitar dasu daga hannun wadannan mutane ubangiji Allah ya kawo musu dauki, domin suna cikin wani hali ubangiji ya dube su mu kuma Allah ya dada kare mu amin!
Yøûsüf ẞæ ßæ Sø
Gaskiya yakamta ace gwamnatin Nijeriya ta jajirice wajen kwato wadannan bayin Alhah da aka sace
Sai dai kuma gashi tana nuna gazawarta a kan haka sai dai mu jajirce da addu’a
Widad Isma’il
Gashi dai har yanzu shiru kake ji, Allah ya jikan maza (Abacha) na yi imanin inda yana raye wannan rashin imanin da halin ko in kula da ake nuna wa talaka ba zai yarda ba koda kuwa baya kan mulki.
Amma shuwagabani ku ji tsoron Allah ku sani Allah ba zai barku ba.
Omar Naseer Imam
Mafitanmu guda daya ne, kuma ita ce madogararmu wato addu’a, gaskiya suna cikin musifa, Allah ya kawo masu mafita albarkan Annabi (S.A.W)
Sani Ladan
Tabbass wannan lamarin ya daure wa mutane kai, yanzu dai takai matsayar hatta magoya bayan gwamnati sun amince ta gaza, haka kuma mu talakawan kasa ya dace mu natsu mu dau matakin addu’a da tashi tsaye don kare kanmu da kanmu tunda gwamnati ta kasa muna addua’r Allah ya kubutar dasu, mu dake gidajenmu Allah ya shiga tsakanin mu dasu.
Abdurrashid Ahmad Abubakar
Lamarin sai addu’a, amma duk wani mataki da yakamata a dauka gwamnati ta sani kuma tana ji, sai dai muce Allah ubangiji ya basu Ikon kubuto da mutanen nan, Allah Ya kara kiyayemu
Sameenu Reina Dambatta
Allah ya kawo wa talakan Nijeriya mafita
Idriss Aminudeen
Ai matakin kenan mu kara kaimi wajen yi musu addu’a, amma indai gwamnati muke jira su dauki mataki to mun makara. Allah ya kubutar dasu
Mujitaba Suleiman
Allah ya hada yan ta’adda fada tsakanin su da masu daukar nauyinsu
Nazifi Haruna Iliyasu
Ai sai dai nace Allah ya fitar dasu daga hannun wannnan ‘yan ta’addan domin kuwa gwamnati ta gaza baza ta iya ba.
Bello Bello
Kaicho rayuwar talakan Nijeriya abin tausayi, Allah ya kawo mana dauki
Maman Aisha
Allah ya kawo mana dauki ya kubutar dasu Allah ya saka musu wannan zaluncin
Ummu Ibrahim
To ni abin da yake bani mamaki ta yaya suka tsayar da jirgin kasar har suka kwashe mutanen
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Wannan al’amari babu wani mataki da Gwamnati za ta iya dauka face mu yi ta addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan fitina don ta nuna mana ta gaza.
Amma maganar gaskiya gwamnatin Nijeriya ba za ta iya bawa al’umma kariya daga rashin tsaro da yake afkuwa ba.
Shamsi Umar Bakanike Dambatta
Da farko dai mu dage da addu’a dare da rana duk lokacin da mu kayi sallah bawai sai abu ya faru ba muce kai ai wannan abin sai dai addu’a kuma baza mu yi addu’a ba kamar yadda muke fadin idan abu ya faru muke cewa ai abin sai dai addu’a da addu’ar muke yi haka da tuni mun samu mafita a wajen Allah [S.W.T] da fatan al’umma zamu tsaya mu zage dantse wajen yin addu’a dare da rana a kan Allah [S.W.T] ya kawo mana karshen wannan matsala na rashin tsaro da ya addabi wannan kasa tamu Nijeriya dama duniya baki daya.
Sani Bello Kano
Abin akwai ban tausayi da bakin ciki, ita kuma wannan gwamnatin sai dai mu yi ta addu’a, saboda inda ace gwamnati tana da niyar kawo karshen rashin tsaro da tuni abin ya zama labari, amma kullum sai maganar siyasar suce a gaban su, ai sun san inda ‘yan ta’addan suke da zama ba wai basu sani ba, Allah shi ne zai mana maganin duk wani ciwo da yake damun mu, su kuma Allah ya kawo musu mafita
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya ra’ayina shi ne yakamata ace gwamnati tunda ta gaza karbosu to ta bawa iyalasu damar biyan kudin fansar don su fanshi iyalansu