Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ya ce ya gano karin wasu hanyoyi da ake satar danyen man fetur a kasar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a shafukan sada zumunta, NNPC ya ce ya gano wasu hayoyin bututun mai 33 da haramtattun matatun man fetur 220.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Asibitin Ƙauran Namoda Da Ya Inganta
- Zulum Ya Raba Wa Magidanta 10,000 Kayan Abinci A Mafa
“Cikin mako guda mun gano haramtattun hanyoyi 33 na bututun mai da haramtattun matatun man fetur 220.”
Wannan na zuwa kwana daya bayan da NNPC ya ayyana samun ribar Naira tiriliyan 3.3 a 2023.
Kazalika, lamarin na faruwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man fetur da gwamnati Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta cire a bara, amma kuma wasu rahotanni ke zargin ana ci gaba da biyan kudin ta bayan fage.
Sai dai NNPC ya ce kudaden da ake ikirarin an biya ba na tallafin mai ba ne duk da rahoton da ruwaito cewa Tinubu ya ba kamfanin na NNPC umarnin ya biya wasu kudade a matsayin na tallafin man fetur.
Sai dai kuma a yanzu haka ana fama da matsalar karancin man na fetur, inda ake ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.