Rahotanni sun ce, an kashe ‘yan bindiga da dama da kuma wasu sojoji yayin wani artabu a kauyen Gudiri da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase ta jihar Filato.
Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan da sojoji suka tsinci gawar wani dansandan da aka yi garkuwa da shi a ranar Larabar makon jiya a kewayen kauyen Kampani da ke gundumar Bashar a wani daji.
- Ƴansanda Sun Kuɓutar Da Mutane 7 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Katsina
- Philippines Ta Zamo Mai Tada Zaune Tsaye A Yankin Tekun Kudancin Sin
Mazauna unguwar sun shaida wa Daily Trust cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, inda sojoji da ‘yan banga suka kai wa ‘yan bindigar farmaki har maboyarsu.
Sun kara da cewa, jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar daga maboyarsu.
Mazauna yankin sun ce, an kwato shanu fiye da 100 daga hannun ‘yan bindigar da ake zargin sato su suka yi.
Kakakin rundunar soji ta ‘Operation safe Haven’, da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Samson Zhakom, bai amsa kiran waya ba a lokacin da aka tuntube shi.
Shafi’i Sambo, shugaban matasa a Wase, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, ba zai iya tantance adadin wadanda suka mutu a yayin artabun ba, amma yana kyautata tsammanin an kashe ‘yan bindiga da dama duk da cewa, wasu sojoji sun rigamu gidan gaskiya.