Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Abdulaziz Yari a ranar Laraba, ya bayar da tallafin tirela 15 na hatsi iri-iri ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Gummi.
Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Mai Martaba Sarkin Gummi, Mai Shari’a, Lawal Hassan (mai ritaya).
- Ɗan Sarkin Gobir Da Aka Kashe Ya Kuɓuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga
- Za A Gudanar Da Bikin CIFTIS Na Shekarar 2024 A Birnin Beijing
Tsohon gwamnan Zamfara ya kuma bayar da tallafin katifu 5,000 da barguna 10,000 ga wadanda abin ya shafa.
In ba a manta ba, Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rahoto cewa, mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya kwashe kusan sa’o’i 14 a ranar Juma’a yana sauka, ya lalata gidaje kimanin 2,795 a garuruwan Gayari, Falale da Gummi, da dai sauransu.
NAN ta kuma rahoto cewa, an rasa rayuka 16 da gonaki da ba a tantance adadinsu ba, duk sun nutse cikin ruwan.