Wani mai tsayi mita 1.4 da wani na daban mai tsayi mita 1.9 suna iya zama abokan wasan kwallon kwando a filin wasan kwallon kwando? Matashi daga garin Xixiang na birnin Hanzhong na lardin Shan’anxi na kasar Sin Hu Yan, shi ne mutumin din mai tsayi mita 1.4.
A shekaru 7 da suka gabata, Hu Yan mai tsayi mita 1.4 ya buga wasan kwallon kwando tare da dan wasan kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Sui Ran mai tsayi mita 1.9 a wani gasar wasan da asusun Yao ya gudanar, tun daga lokacin, Hu Yan ya fara kaunar wasan kwallon kwando.
A lokacin zafi na shekarar 2015, asusun Yao na kasar Sin yana son zabi yara guda 17 daga yankuna masu fama da talauci don samar musu damar buga wasan kwallon kwando tare da ‘yan wasan kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin da na kungiyar wasan wato NBA ta kasar Amurka, Hu Yan mai shekaru 10 yana daya daga cikinsu. A lokacin, Sui Ran da Hu Yan suna cikin kungiya guda, Sui Ran ya ce a lokacin Hu Yan ya fi gajere a cikin dukkan mutane masu halartar gasar.
Amma lokacin da aka fara gasar, Hu Yan ya baiwa Sui Ran ban sha’awa sosai. Koda yake Hu Yan ya koyi buga wasan kwallon kwando har na rabin shekara kawai, amma ya iya buga wasan kamar jigon kungiyar a gasar. Sui Ran ya taimakawa Hu Yan a gun gasar, don haka wannan mutum mai tsayi mita 1.9 da Hu Yan mai tsayi mita 1.4 sun zama abokan wasan a gun gasar. Bayan da Hu Yan ya zura wani kwallo a cikin raga, membobin kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin dake kallon gasar sun yi tsalle don taya murna ga Hu Yan. A ganin Hu Yan, a lokacin ya yi tamkar wani tauraron wasan.
Wannan lokaci, lokaci musamman ne ga Hu Yan domin ya fara kaunar wasan kwallon kwando. Daga baya kuma, Hu Yan ya kan buga wasan kwallon kwando a makaranta, da zama dan wasa mai kyau a cikin kungiyarsa ta makarantar. Kana shi da sauran yara masu halartar gasar wasan kwallon kwando da asusun Yao ya gudanar sun zama abokai har ma zama abokan wasan kwallon kwando. Wasan kwallon kwando shi ma ya taimakawa matashi Hu Yan wajen kwantar da hankali yayin da yake fuskantar matsaloli a zaman rayuwarsa.
Hu Yan yayi zaman rayuwa tare da mahaifinsa da kakanninsa da kuma dan uwansa. Mahaifin Hu Yan wato Hu Wanxia yana aikin gyaran keken babur a garin, ya kan tashi aiki da sasafe da koma gida da daddare. A lokacin hutun karatu, Hu Yan ya kan fita waje don buga wasan kwallon kwando tare da abokansa, yana morewa buga kwallon kwando tare da su. Hu Wanxia ya ce, Hu Yan ya samu babban canji bayan ya fara buga wasan kwallon kwando, ya canja zuwa mai jin farin ciki. Koda yake ana fuskantar talauci a gidan Hu Yan, amma mahaifinsa Hu Wanxia ya kiyaye nuna goyon bayan Hu Yan wajen buga kwallon kwando. Hu Wanxia ya bayyana cewa, a lokacin ya zama matashi, shi ma yana son wasan kwallon kwando, amma ba shi da dogo kana ba shi da kudi, yanzu yana son goyon bayan dansa.
Amma a shekarar bara, an gano ciwo mai tsanani kan kakan Hu Yan, ana bukatar kudi da dama wajen bada jinya gare shi. Batun ya kawo babbar illa ga karatun Hu Yan da kuma halin zuciyarsa. Hu Yan bai shiga jami’a ba, ya tafi birnin Xi’an don koyon ilmin fasahohin kamfuta. Ba a samu filin wasan kwallon kwando a kewayen sabon wurin kwanta na Hu Yan ba, don haka ya dakatar da buga kwallon kwando. Amma mahaifinsa Hu Wanxia ya kiyaye sa kaimi ga Hu Yan ya halarci gasar wasan. Ya ce koda yake akwai matsaloli a cikin gida, amma ya damu da dansa ya rasa abin da ya kauna.
A lokacin, asusun Yao ya yi shirin live ta yanar gizo, Sui Ran wanda ya zama mai kula da harkokin wasannin motsa jiki a yanzu ya shiga shirin, inda ya tuna da Hu Yan, shima aka gayyace shi a cikin shirin din.
A halin yanzu, Hu Yan ya zama baligi, kana Sui Ran ya canja matsayinsa daga dan wasan kwallon kwando zuwa mai kula da harkokin wasannin motsa jiki. A yayin shirin live, Sui Ran ya san kakan Hu Yan ya samu ciwo mai tsanani, saidai ya tsaida kudurin bada kudin kyauta Yuan dubu 10 ga gidan Hu Yan, kana ya yi alkawarin goyon bayan Hu Yan don gama karatunsa.
Sui Ran ya bayyana cewa, ya san Hu Yan yana kaunar wasan kwallon kwando, amma ba shi samu damar taka hanyar buga wasan. Amma Hu Yan yana da halaye mai kyau, zai samar da gudummawarsa a duk wane bangare da zai yi aiki.
Mahaifin Hu Yan wato Hu Wanxia ya san wannan lamari, saidai ya rubuta wata wasika don nuna godiya ga Sui Ran. Kana Sui Ran shi ma yana godiya ga sake gamu da Hu Yan, ya bayyana cewa, asusun Yao ya kiyaye taimakawa wadannan yara kamar Hu Yan, shi ma yana kulawa da ‘yan wasa da su kara samun ci gaba. Asusun Yao ya gayawa kowane dan wasan cewa, ba ma kawai su buga wasan domin kansu ba, hatta ma ya zama misalai ga yara masu son wasan.
Tsohon masahurin dan wasan kwallon kwando na kasar Sin Yao Ming ya kafa asusun Yao a shekarar 2008, burin asusun shi ne horas da yara da tsamo masu hazaka a fannin wasannin motsa jiki. Asusun Yao ya dukufa wajen horas da wasannin motsa jiki, da kiwon lafiyar jikin matasa da yara. Ta hanyar nuna goyon baya ga ayyukan raya matasa da yara kyauta, asusun Yao ya sa kaimi ga mutane da dama maida hankali ga matasa da yara da suke rayuwa a yankuna masu fama da talauci, ta yadda za a taimaka musu wajen samun ci gaba a fannonin ilmi, da wasannin motsa jiki, da kiwon lafiya da sauransu.
Muhimman ayyukan da asusun Yao ya gudanar, sun hada da aikin gina makarantun firamare a yankuna masu fama da talauci, da shirya gasannin wasan kwallon kwando, da shirin horar da malaman wasannin motsa jiki a kauyukan kasar Sin. Matakin da ake fatan zai taimaka wajen daidaita matsalolin rashin malaman koyar da wasannin motsa jiki, da kwasa-kwasan wasannin motsa jiki, da ayyukan wasannin motsa jiki a makarantun kauyukan kasar Sin, ta hanyar tura masu aikin sa kai zuwa kauyuka, da bada ilmi a fannin wasannin motsa jiki, da horas da fasahohin wasan kwallon kwando, da gudanar da gasanni da dai sauransu, ta yadda karin daliban makarantun kauyukan kasar Sin za su samu ci gaba wajen halartar wasannin motsa jiki.
Hakazalika, a shekarar 2019, asusun Yao ya fara aiwatar da shirin horar da malaman wasannin motsa jiki a kauyukan kasar Sin, wanda ya maida hankali ga inganta karfin malaman wasannin motsa jiki dake aiki a makarantun kauyukan kasar Sin. Ya zuwa yanzu, akwai malamai guda 100 dake cikin shirin, wanda daga karshe, zai kai ga magance matsalar karancin malaman wasannin motsa jiki dake ake fuskanta a makaratun kauyukan kasar.
A cikin shekaru da dama da suka gabata, asusun Yao ya kiyaye yin kokarin kyautata tsarin wasannin motsa jiki a kauyukan kasar Sin. Asusun ya riga ya gudanar da gasar wasan kwallon kwando ta makarantun firamare karo sau 10 don sa kaimi ga yaran makarantun firamare da su fara son wasan kwallon kwando da samar musu damar shiga wasannin motsa jiki.
Ya zuwa karshen shekarar 2021, asusun Yao ya riga ta tura masu aikin sa kai 3826 zuwa makarantu fiye da 2400 na larduna da yankuna 29 na kasar Sin don bada ilmin wasannin motsa jiki da bada horaswa da kuma gudanar da gasanni, don haka yara da matasa fiye da miliyan 2 da dubu 710 sun samu damar yin wasannin motsa jiki ko samun ilmi da horaswa.
Kana asusun Yao ya riga ya gudanar da gasar wasan kwallon kwando karo sau da 10, ‘yan wasan kasar Sin da na kasar Amurka fiye da 200 sun halarci gasar. Kana shirin live na aikin sa kaimi ga yara masu zaune a yankuna masu fama da talauci da su fara buga wasan kwallon kwando ya kan samu kurin kyauta daga mutane da dama a kowace shekara, Sui Ran yana daya daga cikinsu.
Sui Ran ya ce, ya shiga dandalin wasannin motsa jiki har na tsawon shekaru da dama, ya gano cewa, wasanni yana taimakawa horar da mutane a fannoni daban daban a cikin zaman rayuwarsu. Ban da Hu Yan, Sui Ran yana fatan zai taimakawa karin mutane a wannan fanni. Wasanni zai kawo tasiri ga zaman rayuwar mutum sannu a hankali, Sui Ran yana son kallon ko akwai canji a nan gaba.
A ganin Hu Yan, akwai sauran doguwar rayuwarsa. Ban da wasan kwallon kwando, ya fara koyon ilmin fasahohin kamfuta. Yana fatan ta hanyar yin kokari, zai iya tafe waje don ganin wuraren waje da idanunsa.
Zaman rayuwarsa na buga wasan kwallon kwando ya zama karfi a cikin zuciyarsa, Hu Yan ya ce, ya taba buga wasan kwallon kwando tare da ‘yan wasan kungiyar wasan ta kasar Sin, ya iya daidaita matsalolin da yake fuskanta a halin yanzu, zai samu kyakkyawar makoma a zaman rayuwarsa a nan gaba. (Zainab Zhang)