Ana samun ko karuwa da ilimi ne idan an samu yin wata mu’amala tsakanin mai koyo da wani lamari , sai kuma gudunmawar da malami ya bada wajen samar da yanayin, ta haka ne kuma shi mai koyo zai nuna ya koyi abin da ganewa, daganan shi ma sai ya yi mu’amala da su (Al-Kaisi, 2015).
Wadannan sabbin abubuwa a lamarin koyarwa tare da ci gaban da aka samu ta bangaren fasaha su suka bada gudunmawa wajen samar da dabarun koyarwa.Dabarun koyarwa wadanda aka fi amfani da su da kuma yadda suke sun hada da wadannan kamar haka : (Al-Nuaimi, 2012).
- An Ceto Ɗalibai 20 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Binuwe
- Mutum Miliyan 7.9 Da Ta’addanci Ya Tagayyara A Jihohi 3 Na Bukatar Agaji – UNOCHA
Na farko: Nau’in dabarar koyarwa saboda irin ilimin da ake koyo irin wannan dabarar koyarwar, ita ma ta kasu kashi uku wato:
cognitive domain, emotional domain, psychomotor domain. suma din an raba su gida uku.
A. Nau’oin koyarwa ta hanyar bayyana hujjoji da dalilai ta hanyar da kuma abinda, za a cire, bincike, ko kuma wani abinda ba sani ba.Amafani da wadannan nau’oin binciken mutane uku ne da suka hada da Piaget, Brunner, Ausubel,da sauran masoya nau’in karatu ta yadda dalibai za suyi amfani da kwakwalwarsu wajen koyo, su suka bada kwarin gwiwa na amfani da su.
B. Dabarun koyarwa saboda kudurin da ake niyyar cimmawa da kuma hanyar da za a bi.
C.Dabarun koyarwa ta hanyar cigaban da ake sa ran samu.
Na biyu:Bayanin koyarwa na dabarun da ke alaka da ilimin na yadda al’amari yake.
Wadanda suke ganin wannan dabarar tana amfani sun ce kowane bangare na koyon ilimi yana da wani abu na musamman dake bukatar yin amfani da dabarun yin bincike da tunani wadanda suka sha bambam daga sauran.Ta hanyar fahimtar dabarun koyarwar sai aka raba su a karkashi nau’oi uku (Al-Nuaimi,2012)
A. Dabarun koyarwa na kimiyyar zahirance:Dabarun na kimiyya kamar dabaru ne kamar dabara ta bincike na daga cikin muhimman dabarun da aka yi amfani dasu ta wannan sashe.
B. Dabarun koyarwa na saboda al’umma da kimiyyar dan Adam,su wadannan dabarun na da alaka ne wajen maida hankali ne akan mu’amala tsakanin ‘yan Adam.Alal misali dabarar yin magana da kuma ta wasa.
C. Dabarun koyarwa na kimiyyar da za a iya amfani da ita: Wadannan dabarun na nuna sha’awa ta kimiyyar da za a yi amfani da ita, misali ana shi ne dabara ta rubutu akan wani maudu’i.
Na uku. Bayanin dabarar koyarwar data shafi
gudunmawar da malami da wanda ake Koyawa ma: wannan dabarar ita ce aka fi amfani da ita a tsakanin masana ilimi a duniya,ta kuma danganta ne ta hanyar raba dabarun koyarwar gida biyu (Al-Nuaimi, 2012):
A. Dabarar koyarwa a gargajiyance wadanda a takaice ne,dabarun gabatarwa da, amincewa da abinda aka koya,babban matakin shine gudunmawar da mlami,da kuma mai koyo wadda take ta biyu ce.Wadannan dabarun sune dabarun koyarwa da aka dade ana amfani da su,da suke kallon samun ilimin wanda dama bukatar ke nan,ba kamar halin da ake ciki yanzu ba wanda ana bukatar sai an samu ilimin,a matsayin wata hanya ce da za a cimma wani buri. Ta hanyar dabarar koyarwa ta gargajiya a makaranta, malamai na amfani da ita wajen hukunta masu koyo su nemi labari da kuma adana shi, ba tare da mai da hankali ba kan abinda suke so da inda suka sa gabansu.
B. Dabarun koyarwa na zamani: anan shi mai koyo shi ne babba wanda yake bada gudunmawa, yayin da shi kuma malamai an bar shi wajen bada shawara yadda za ayi,duba yadda ake yi, da kuma bada shawara.Maganar gaskiya samun bullowar dabarun ba wai sun zo bane a matsayin su yi maganin wadanda ake yi a gargajiyance wato na da ke nan,sai dai a matsayin wata hanya ce ta bunkasar ilimi.Ta wata hanya kuma, wajen amfani da tsare- tsaren da aka yi n zamani.Idan har dabarun koyarwa a gargajiyance basu ga muhimmancin mai koyo ba ta lamarin koyarwa,sai dai kuma dabarun koyarwa na zamani sun bada ko maida hankalinsu kwarai da gaske akan shi mai koyon,abubuwan da yake so,da bukatun sa sune akan gaba in ana maganar hanyoyin koyo, dokokinsu,da kuma yadda za a cimma muradin.Misalan dabarun koyarwa na zamani wadanda za a iya amfani da su ta hanyar amfani da darasin Larabci sun hada ta yin rubutu kan wani maudu’i, bincike, maganin matsala, tattaunawa, sassa da gudunmawar da ake badawa,sai kuma yin ayyuka.Wajen kulawa da wadan can dabarun ana iya gane cewa suna amfani ne da hanyoyin lamurran ilimi na zamani da suke bada gudunmawa, ta wajen shiryawa da gyarawa, domin a samu ganewa da fahimtar mai koyon ta yadda abin zai amfane shi sosai.Wadannan abubuwan sun hada da.