Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai kawo muku yadda za ku gyara gashinku yayai kyau da laushi yayi santsi.
Gyaran Gashi 1
Kayan Hadin;
Man Zogale, Man Kwakwa, Man Zaitun:
Yadda za ku hada:
Za ku tanadi wadannan mayukan da muka ambata sai a hade su waje daya ki rinka shafawa a kai. Yana gyara gashi ya mikar da shi ya yi laushi.
Gyaran Gashi 2
KAYAN HADI:
Man zogale, ganyan Magarya, Kanunfari kadan
Yadda za ku hada:
Idan kika tanadi wadannan mayukan da muka ambata sai ki hade su waje daya ki rika shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi.
Gyaran Kafa:
Ba ke ba zuwa wajen wanke kafa matukar kin yi amfani da wannan hadin:
Kayan da zaku tanada:
Man Shanu Man Kwakwa, Man Ridi, Man Alayyadi:
Yadda za ki hada:
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi, da daddare za ki hada wadannan mayukan da muka ambata waje daya ki shafa a kafa in za ki kwanta bacci daddare, sai ki daure da leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi. Idan kina yin haka da yarda Allah kafarki za ta yi kyau.
Maganin ciwon sanyi:
Duk macen da ta ke son ni’ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni’ima to lallai ya zama dole ta magance matsala ciwon sanyi, domin magance wannan matsala ta samu wadannan kayan;
Hulba, Bagaruwa, Habbatussauda:
Ki hada Hulba da Bagaruwa waje daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man Habbatussauda ki yi matsi da shi.