Wani kwararren likita a Nijeriya, Dakta Ben Ahunonu; ya gargadi ‘yan Nijeriya kan amfani da kayan marmarin da aka jima da yankawa da ake sayarwa a kan hanya.
Likitan ya kara da cewa, wadannan kayan marmari da suka hada da Abarba, Gwanda, Kankana da sauran makamantansu; ana yankawa ana sayarwa a kan titina da sauran hanyoyi, wadanda kuma sanin kowa ne kwari kamar irin su Kuda na bin su; a duk ire-iren wadannan gurare da ake gudanar da wannan sana’a.
“Yanka ire-iren wadannan kayan marmari ana sayarwa, na tattare da matsaloli da dama; musamman ganin cewa ana yanka kayan itatuwan su jima kafin a yi amfani da su, wasu tun safe ake yankawa; haka za su kai har dare, wasu ma su kwana su kara kwana; sannan a haka za a sayarwa da mutane.”
Saboda haka a cewar tasa, akwai wasu kwayoyin cuta da ke tattare da irin wadannan kayan marmari; sakamakon barin su da ake yi su jima a ajiye bayan an yanka su.
“Kudajen da ke bin wadannan kayan marmari, na iya kasancewa ko dauke da wasu kwayoyin cuta; wadanda ka iya haifar da wasu cututtuka kamar; gudawa, ciwon zazzabi (typhoid) da kuma cutar kwalara”, a cewar Daktan.
Don haka, sai ya ba da shawarar cewa; cin dukkanin ‘ya’yan itatuwa ko kayan marmari, abu ne da ya kyautu a kula da shi tare da yin nazari sosai; musamman ta fuskar sanya kudi wajen saya da kuma yin la’akari da amfaninsa a jiki.
“Saboda galibi bayan an yanka su; iska ta gama ratsa jikinsu, babu wuya suke fara daukar hanyar lalacewa.
“Mafi yawan mutane, ba su da ilimin cewa; bawon jikin ‘ya’yan itatuwa su ne ke kare dukkanin abin da ke cikinsu, da zarar an yanka; babu kuma abin da zai kare abin da ke ciki. Shi yasa ake ba da shawarar cewa, ka da a yanka sai an tashi amfani da shi”, in ji shi.
Saboda haka, ya sake shawartar mutane da cewa; duk yayin da suka tashi sayen kayan marmari, wajibi ne su duba tare da tabbatar da cewa; bai lalace ba. Dalili kuwa, dukkan kayan marmari masu kyau; wadanda kuma aka yanka nan take, su ne ke da amfani tare da gina jiki.
Har ila yau a cewar likitan, kayan itatuwar da aka riga aka yanka; amfaninsu na raguwa idan ba a yi amfani da su nan take ba. Ma’ana, idan aka yanka aka bari suka dauki wani tsawon wani lokaci ba a ci ko an sha ba, amfaninsu na samun koma baya; idan aka kwatanta da wanda aka yanka, aka yi amfani da shi nan take.
Haka nan, idan aka ji ya fara canzawa ta fuskar dandano ko warinsa; a nan ya zama wajibi a zubar da shi, ka da a yarda a ci ko a sha.
A karshe, ya yi nuni da cewa; idan so samu ne, gwara mutum ya sayi kwallon kayan itatuwar da yake bukata; amma sakamakon matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu, mutum zai iya tsayawa ya kula sosai da yanayin wurin da zai sayi wanda aka yanka din tare kuma da duba nagartar wanda zai saya.