Ma’aikatar kudi ta kasar Sin da ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta kasar sun ware Yuan miliyan 50 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7 don tallafawa ayyukan agaji, sakamakon ambaliyar ruwa a lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin.
Za a yi amfani da kudaden ne don muhimman ayyukan gaggawa, da suka hada da ayyukan bincike da ceto, da sake tsugunar da mazauna wurin da abin ya shafa, da kuma rage hadurran da ke da alaka da ambaliya.
Kasar Sin ta kaddamar da shirin ba da agajin gaggawa na matakin-IV a lardin Liaoning sakamakon ruwan sama da ta haddasa ambaliyar ruwa. (Yahaya)