Wasan bidiyo gem na kasar Sin mai suna “Black Myth:Wukong” ya yi matukar daukar hankalin duniya, inda aka sayar da kwafi miliyan 10 a duk fadin dandamalin wasanni a cikin kwanaki uku kacal da fitarwa, a cewar Game Science makerin wasan a daren jiya Juma’a.
A matsayin wasan bidiyo gem mai matsayin “Triple-A” kirar kasar Sin na farko, “Black Myth: Wukong” ya kasance kan gaba a jerin “wasanni da aka fi bugawa” a manhajar Steam, babban dandalin wasannin bidiyo gem, sa’a guda bayan kaddamarwa a safiyar Talata.
- Kasar Sin Ta Kara Ware Kudaden Agajin Gaggawa Ga Lardin Liaoning Dake Arewa Maso Gabashin Kasar
- Shin Barcelona Da Atletico Madrid Zu Su Iya Dakatar Da Real Madrid A La Liga?
Game Science ya bayyana cewa adadin yan wasa da suka buga wasan a lokaci guda ya taba zarce miliyan 3.
Babban littafin tarihin kasar Sin mai suna Tafiya zuwa Yamma wato Journey to the West a Turance shi ya tsima wasan “Black Myth: Wukong”
An yabawa wasan bisa kyawawan al’adu da ka’idodin wasan bidiyo gem na zamani da ke cikin wasan, kuma ya zama abin ban sha’awa da ya yi fice a cikin al’ummar masoya wasannin bidiyo gem. Wannan nasarar da ba a taba yin irinta ba ta kara habaka farashin hannayen jari na wasu kamfanoni tare da zaburar da yawon bude ido a lardin Shanxi, daya daga cikin muhimman wuraren daukar bidiyon wasan. (Yahaya)