Daya daga cikin manyan jarumai dattawa a masana’antar Kannywood wadanda suka dade ana damawa da su a wannan masana’antar Tanimu Akawu ya yi karin haske a kan yadda fina-finai masu dogon zango da suka mamaye masana’antar suke kawo cikas ko kuma koma baya ga ita kanta wannan masana’antar ta Kannywood duba da cewar yanzu zamani ya canza ba kamar shekarun da suka shude ba.
Jarumin a wata hura mai tsawo da ya yi da jarumar Kannywood Hadiza Aliyu a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show ya tabo bangarori da dama da suka shafi wannan masana’antar da ya ce ya shafe shekaru 20 a cikinta.
- Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Harkokin Tsaro Jake Sullivan Zai Ziyarci Kasar Sin
- Babu Tsaftatacciyar Masana’antar Shirya Fina-finai Kamar Kannywood A Duniya -Tijjani Asase
Da farko dai Tanimu ya karyata mutanen da suke daukarsa a matsayin mai satar fasaha (Piracy) a masana’antar Kannywood inda ya ce tun kafin ya fara fitowa a matsayin jarumin fim shi mutum ne da yake harkar gidajen sinima, inda yake sayen fina-finai daga masu sayarwa kokuma shiryawa shi kuma ya nuna a gidan sinima domin neman halalinsa.
Dangane da maganganu da suke tasowa a masana’antar akan cewa akwai wadansu jarumai da suke butulcewa masu gidajensu a masana’antar bayan sun fara samun daukaka ko kuma rufin asiri, Akawu ya ce wannan maganar gaskiya ce domin kuwa shi kan shi akwai da dama a cikin jarumai da furodusoshin da ya taimakawa a lokacin da suke neman taimako amma yanzu bayan sun samu daukaka su kuma suka butulce masa.
Dattijon ya kara da cewa duk da yanzu zamani ya canza mafi yawancin furodusoshi sun fi bukatar shirya fina-finai masu dogon zango sun daina shirya gajerun fina finai,amma wannan ba ita ce hanyar da za ta ciyar da Kannywood gaba ba hasali ma babban koma baya ne ga masana’antar domin kuwa ta wannan hanyar ba kowane fim ne za a yi shi a kammala kuma a samu wani abin kirki na riba ba.
Domin kuwa harkar sinima ita ce kadai hantar da mai shirya fim zai samu kudaden da zai cire uwa kuma ya cire ribar shi cikin lokaci, ba yanzu da wayoyin hannu da sauran kafafen talabijin da suke nuna fina-finai kyauta ba, saboda yanzu zaka dora fim a yanar gizo mutane (‘yan downloading) su saka data da Naira 100 su dauko shi su dinga tura wa mutane akan Naira 10 Naira Ashirin ba tareda ka samu ko Kwabo ba a wajensu.
Haka kuma akwai da yawa a cikin gidajen talabijin da suke nuna fina-finai a kyauta ba tareda ka saka ko sisi ba don haka mutane sun fi zuwa inda za su kalli fim a kyauta ba tare da sisin su ya yi ciwo ba, har ma a kwanaki akwai wata kafar talabijin da ta yi ikirarin daina saka fina finai a kyauta a tashar ta,amma bayan shawarwari sai aka ce mata muddin ta daina nuna fina finai a kyauta za ta yi asarar miliyoyin abokan huldarta hakan ya sa ta fasa, in ji Tanimu.
Da aka tambayeshi wani irin tasiri role din da yake hawa na mugun mutum a masana’antar Kannywood yayi a rayuwarshi Tanimu ya bayyana cewar gaskiya wannan role din ya saka mutane da dama suna yi ma shi daukar mutum mai mugunta a zahiri,inda har wasu ba su iya hada ido dashi don tsoron kar ya cutar dasu musamman mata.
Hakan ya sa nake ganin mutanenmu basu waye wajen kallon fim ba domin suna daukar abin kamar da gaske akeyi,kokuma halayyar da mutum ya nuna a cikin fim haka abin yake a waje wamda ko kusa ba haka abin yake ba sau da dama ka kan samu jarumi mai tausayi ko Imani a cikin fim amma ka same shi akasin haka a zahiri,haka kuma ka kan samu mutum marar imani a cikin shirin fim amma ka samu akasin haka a zahiri kamar dai ni kenan.
Da yake karin haske a kan abinda ya sa kwana biyu a daina ganinsa a fina-finai kamar yadda yake fitowa a baya, Tanimu ya bayyana cewar har yanzu yana sha’awar harkar fim duk da dai cewa ta fara isar shi amma rashin samun wata tsayayyar sana’ar ya sa har yanzu yake a Industry.Dangane da daina ganin sa a fina finai kuwa ya ce shi bai dauki sana’ar fim ko ayi ko a mutu kamar yadda wasu suke daukar ta ba.
Hakan ya sa idan masu shirya fina-finai (Furodusoshi) suka nemi ya zo su yi aiki tare da shi zai zo amma idan basu neme shi ba, shima ba zai tafi wurinsu ya na kamun kafa a kan su saka shi a fim ba, daga karshe Tanimu Akawu ya tabbatar da cewar harkar fim ta yi mashi riga da wando domin kuwa ta sanadiyar wannan sana’a mutane da dama suka sanshi kuma shima ya san mutane da dama.
Kuma yanzu haka yana fadada hanyar neman abincinsa ta hanyar tallace-tallacen ‘yan siyasa da sauran kamfanoni masu bukata, inda ya ce da ba dan wannan sana’a ta shi ta fim ba da bai samu wannan daukakar da mutane suke ganin yana da ita har suke bashi tallace-tallace ba.