Tsohon shugaban jam’iyyar APGA na kasa, Sanata Victor Umeh, ya koma Jam’iyyar Labour.
Sanata Umeh, ya kuma zama dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a mazabar shiyyar Anambra ta tsakiya a zaben 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar Labour na daya daga cikin Jam’yyun da za a buga da su a kakar zaben 2023 mai zuwa idan Allah ya ara mana ran ganin zaben.