Gwamnatin jihar Bauchi ta aike da saƙon gayyata kai tsaye ga fitaccen malamin addinin musulunci da ke jihar Kano, Dakta Abdallah Gadon-Ƙaya domin yi mata ƙarin haske kan jawabin da ya yi da ke cewa, akwai wasu masu shirya luwaɗi da maɗigo a wani otel da ke jihar Bauchi.
Shi dai Dakta Gadon-Ƙaya ya fito a wani faifan bidiyo inda ya ke sanar da duniya cewa, wani ya kirasa a waya ya shaida masa cewa, akwai wani otel da aka ɗauki hayarsa na tsawon kwanaki da kuɗi da ya kai miliyan 100 domin yin maɗigo da luwaɗi da auren jinsi a jihar Bauchi, inda ya ce, masu aikata hakan sun fito ne daga jihohi daban-daban domin sheƙe ayarsu. Har ma ya ce idan ana buƙata zai bada sunan otel ɗin.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Takwas A Karamar Hukumar Birnin Gwari Ta Kaduna
- Tinubu Zai Kai Ziyara Kasar Sin Domin Haɓaka Tattalin Arziki Da Kayayyakin More Rayuwa
A ganawarsa da ‘yan jarida, shugaban hukumar Shari’a ta jihar Bauchi, Farfesa Hamisu Dass, ya ce, gayyatar ta zama dole lura da girman abun da ake zargin wasu na aikatawa a jihar.
“Tun bayan jin jawabin na babban malamin, hankalin mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da Kwamishinan harkokin addinai da mu kanmu hankulanmu sun tashi. Jihar Bauchi, jiha ce da kowa yasan ba za ta amince da nau’ikan wannan rashin ɗa’ar ba, kowa ya san irin ƙoƙarin da gwamnan ke yi wajen kyautata tarbiyya da ɗa’a a tsakanin jama’a.
“Don haka, jin wannan bayanin ya tada mana hankali sosai. A bisa wannan, mun gayyaci jami’an hotel ɗin da ake zargi da cewa wannan abun ya faru ciki, kuma shi ma malamin mun aika masa da gayyata domin mu gano haƙiƙanin abun da ya faru”
Shugaban ya ce, tunin suka ƙaddamar da bincike da sanya ido a otel ɗin da ma sauran otel da suke jihar domin daƙile dukkanin wani lamari da ya shafi irin wannan.
Sai dai ya nuna takaici kan yadda malamin ya hau lasifika ya kama bayyana irin wannan babban lamarin ba tare da ya ankarar da gwamnatin jihar ba, “Irin wannan zai sanya masu laifin ma su gudu ko su ɓuya. Amma da an sanar mana nan take za mu ɗauki matakin gaggawa.”
Farfesa Dass ya nemi al’umma da su kwantar da hankalinsu inda ya ce, tuni aka ƙaddamar da bincike kuma tabbas in akwai wani batu makamancin wannan to za su ɗauki matakin dakile shi.