Jam’iyyar APC ta yi kira ga dattawan jam’iyyar PDP a yankin arewa maso yamma da su mayar da hankali kan rikicin siyasarsu da kuma magance matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya maimakon dora alhakkin gazawarsu ga karamin ministan tsaro, Hon Bello Mohammed Matawalle.
APC ta bayyana hakan ne karkashin kungiyar matasan jam’iyyar da ke yankin arewa maso yamma.
Shugaban kungiyar, Alhaji Ashiru Tukur ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin cin zarafin da jam’iyyar PDP ta yi wa magoya bayansu a yankin arewa maso yamma da kuma karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
- Ɗan Sarkin Gobir Da Aka Ceto Ya Bayyana Ɗan Siyasar Da Ke Da Hannu Kan Kama Shi
- ‘Yan Siyasar Nijeriya Ne Ke Ta’azzara Rashin Tsaro Don Cimma Wata Manufa Ta Siyasa – Shugabar WTO
Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Tinubu da ya dakatar da karamin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle daga musguna wa shugabannin adawa a yankin arewa maso yamma.
Shugaban ya bayyana cewa zarge-zargen cin mutuncin siyasa ta kowace hanya a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, farfagandar siyasa ce mara tushe da nufin bata sunan gwamnatin APC da ke kan gaba wajen gyara Nijeriya.
Ya bayyana jam’iyyar PDP a arewa a matsayin tarin ‘yan bangar siyasa da ba su da tushe balle makama wadanda suka kulla makircin don haifar da rashin zaman lafiya da haifar da fitina a tsakanin ‘yan Nijeriya.
“Bayan gazawar PDP, sun kasa gudanar da mulki ko da a cikin jihar daya wajen magance talauci da tabarbarewar tattalin arziki hade da rashin tsaro sakamakon sakaci da rashin shugabanci nagari.
“Duk lokacin da PDP ke son boye gazawarta a jihar, za ta yi amfani da farfagandar siyasa. Wannan wata alama ce ta gazawa da raunin da ke da alaka da kiyayyar ‘yan siyasa na zargin kamar minista wajen haifar da tashin hankali, rikici da rashin jituwa a daidai lokacin da mutane ke neman mafita don kawo karshen rashin tsaro, yunwa, da talauci,” in ji Tukur.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu yana son ya raya al’umma mai mutunta juna da fahimtar juna da ci gaba.
A cewarsa, yana da kyau irin wannan shugaba ya nisanci dabarun raba kan jama’a, da samar da tsarin hadin gwiwa mai ma’ana maimakon dumama harkokin siyasa a wani mataki na raba kan al’ummar kasar nan.
Ya ce yana da kyau shugabannin PDP su gaggauta neman afuwa kan wannan farfagandar siyasa.
Jam’iyyar PDP ta zargi APC ta cin zarafin magoya bayanta a yankin arewa maso yammacin kasar nan, wanda ta ce ba iya ba su hakkinsu yadda ya kamata a matsayinsu na ‘yan adawa.