Jami’an rundunar Ƴansanda a jihar Bauchi sun kama wani matashi mai suna Abubakar Talba maih shekaru 37 da haihuwa bisa zarginsa da sace Mas’ud Barau mai shekaru 12 da kuma Ibrahim Kabiru mai shekaru 13 daga Daura a Jihar Katsina.
Hakazalika, ana zargin wadanda aka cafke da yin luwadi da daya daga cikin yaran mai suna Barau, wanda ya fito daga Kauyen Gamniya a Jamhuriyar Nijar a wani masallaci da ke Udubo, al’ummar Karamar Hukumar Gamawa ta Jihar Bauchi.
- NDLEA Ta Cafke Wani Ɗan Kasuwa Ya Haɗiye Hodar Iblis Ƙulli 88 A Abuja
- NDLEA Ta Cafke Wani Ɗan Kasuwa Ya Haɗiye Hodar Iblis Ƙulli 88 A Abuja
Barau ya hadu da Talba ne a Rijiyar Zaki ta Jihar Kano bayan ya yi hijira zuwa Nijeriya domin koyon haddar Alkur’ani mai girma.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar.
Al’ummar Udubo da ke Karamar hukumar Gamawa a Jihar Bauchi sun shigar Talba kara a gaban kotu kan yadda yake musgunawa yaran da ke karkashinsa a matsayin malamin Alkur’ani, tun da farko ya koma garin daga Daura.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya halarci makarantar Alkur’ani a Fagge, inda ya hadu da daya daga cikin wadanda abin ya shafa a unguwar Bata da ke Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
“Wanda ake zargin ya yaudari Barau na farko daga Kano zuwa Daura da cewa zai tallafa masa ya fara sana’a, a kan cewa ya samar da jari don fara sayar da fitilun taba da batura.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike,” in ji Wakil.