Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ranar Juma’a ya ziyarci garin Ilorin na jihar Kwara, domin neman alfarmar Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, domin tabbatar da takararsa ta shugaban kasa.
Kwankwaso ya samu rakiyar dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar NNPP a jihar, Farfesa Shuaib AbdulRaheem, Alh Buba Galadima da kuma dan takarar Sanatan Kwara ta Arewa a jam’iyyar, Dr Kolo Baba, a fadar sarkin.
Da yake jawabi a fadar Sarkin jim kadan bayan idar da Juma’a tare da Sarkin, Kwakwanso ya ce ya je Ilorin ne domin neman tabarrakin masarautar.
Ya kara da cewa zai yi amfani da damar ziyarar wajen bude wasu ofisoshin NNPP a Ilorin babban birnin jihar da sauran sassan jihar.
“Mun zo nan ne don girmamaka a matsayinku na iyayen al’uma, muna godiya da ka karbarmu da kuma bamu damar ganawa da da mu, ina kuma gode wa al’umar jihar da suka nuna mana karamci, muna addu’ar Allah Ya ba mu damar yin hidimar Jama’a tare da ku. Muna ci gaba da Addu’ar Allah ya baiwa Sarkinmu tsawon rai da lafiya,” in ji Kwankwaso.
Da yake mayar da martani, Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana Kwankwaso a matsayin gogaggen dan siyasa kuma kwararre wajen gudanar da sha’anin mulki.
Ya yi addu’ar fatan alheri ga kungiyar Kwankwansiyya, inda ya kara da cewa “Allah zai ci gaba da yi muku jagora, na yi matukar farin ciki, kuma muna maraba da ku”.
A takaitacen jawabinsa, Farfesa AbdulRaheem, wanda ya gode wa Sarkin bisa irin karramawar da kungiyar ta NNPP ta yi masa, ya ce Kwankwaso na da dukkan abin da ya kamata domin fitar da al’umar kasar nan daga matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke fuskantarta.