Da safiyar yau Lahadi ne shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya iso birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, domin halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 wato FOCAC, wanda za a gudanar a birnin na Beijing, kana shugaban na Najeriya zai gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Sin.
Haka kuma, a halin yanzu, akwai wasu shugabannin kasashen Afirka da su ma suka iso birnin na Beijing domin halartar taron na FOCAC, wadanda suka hada da shugaban kasar Guinea Mamadi Doumbouya, da shugaban wucin gadi na kasar Mali Assimi Goita, da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki, da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit, da kuma shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp