1) Ana iya lura da bambance – bambance da ke tsakanin wadanda ake koyamawa ta hanyar kaifin basirarsu, sha’awarsu,da kuma irin abubuwan da suka sani a baya.
2) Ci gaban gaba daya na basirar ganewa ta hanyar ganewa, fahimta,da kuma yin dukkan abubuwan da aka koya.
- Kudirin Wa’adin Shekaru 6 Ga Shugaban Kasa Ya Tsallake Karatu Na Farko
- Har Yanzu Ba A Kammala Kwangilar Dakin Karatu Da Aka Bayar Shekara 18 Ba
3) Samun cimma nasarar da ake so ta ‘yancin kai na mai koyo da kuma yadda Malami yake yi ma shi jagoranci na yadda zai koya.
4) Yin amfani da damar da aka ba masu koyo domin a basu dama ta gane abubuwan da ake koya masu, ta yadda fahimtar lamarin daidai da yadda kwakwalwarsu take domin amfanar da su a gaba.
5) Bada dama ga masu koyo su dauki matakansu da kuma ayyukan da suke tare da matakan da suka dauka.
6) Hada tsarin da ilimin ya kunsa ga shi rayuwar mai koyon, sai kuma ba shi mai koyon kwarin gwiwa ya bayyana manufarsa,da kuma karafafa masa wajen saurare da mutunta shawarar wasu.
Muhimman ka’idoji da ake amfani da su wajen dabarun koyarwa an gina su akan, cewa dabarun koyarwa suna da muhimman ka’idoji, wadanda daga cikinsu sun hada da (Ahmad, 2005):
1.Samun karuwa daga abinda ba a sani ba zuwa ga wanda aka sani:Idan sabbin bayanai suna da alaka da wadanda aka sani ya kasance kuma su dalibai sun san su, don haka ana cewa an fahimci abin ko lamarin.Idan ana maganar darussan harshen larabci, ana iya karuwa da shi wancan salon ko waccan dabarar ta fara koyar da dalibai akan karatu akan hoto wanda ya sani (hoton mahaifi da mahaifiya), har dai a hankali a gabatarwa dalibin wasu alamu da zai gane bai san su ba.
2) Samun cigaba daga mai sauki zuwa mai wahala ko wuya, wannan na nufin abinda dalibi ya gani da sauki ko da wahala.Misali anan shine harshen larabci da ya kunshi koyawa yara wasu haruffa, ko magana da abin ya kunshi jimloli kamar : house gida, head, kai, turn juyawa, daganan kuma sai jimloli kamar: Samir, Saeed, house, da dai sauransu.
3) Samun sauyi na koyo daga gaba daya zuwa wani bangare: Wannan dabarar koyarwar tana amfani ne da halittar halin da hankali yake ciki wajen gane abubuwa.Wanda ya ga itace ko ice gaba dayan shi daga nan kuma ya fara Kallon sassan shi, kamar gangar jikin iccen, rassa, ganyaye,da kuma ‘ya’ya.Misalin wannan shine harshen larabci a karanta maganar ko kalma ,daganan kuma sai ayi nazarinta a harafi da kuma kalmomi.
4) Samun cigaba daga gaskiyar lamari ko wani abu inda za a gani zuwa yadda abin zai sauya:Saboda shi dan makaranta zai gane abubuwa da suke kusa da shi ta wannan hanya,ya san dabbobi da suke a muhallin da yake domin yana kallonsu da farko, sannan kuma a gaba zai rika ganinsu a hoto, wanda har daga karshe zai iya gane ko wadanne bubuwa ne idan ya ji ko ya ambace su ko abin.
Malamai na dogara ne akan dabaru da kuma dabarun da za su isar da ilimin da suke da shin a wani abu,dabaru,da kuma labari zuwa ga dalibansu, abinda zai kai ga sa yin tunani da abinda zai biyo baya.Ko wacce dabara tana da nata amfani, yadda za a yi ta, da kuma dokoki.Malami shine zai tsara kan abinda ya yi nazari,yadda zai gabatar da abin ga dalibai ta yadda za su gane.A kwai dabaru inda su ma ‘yan makaranta suke bada gudunmawa tare da Malaminsu wajen koyon wasu hanyoyi, da kuma gane abinda ake koya masu, wato kamar dabarar gabatarwa da kuma hanyar da ake tattaunawa. Wadannan dabarun suna taimakawa ‘yan makaranta wajen yiyuwar abinda suke so da sha’awarsu, yayin da shi kuma Malami zai kasance wajen yin amfani da dabarar shi da ta taimaka wajen yin muhawarar da kuma tattaunawa.Ilimi ya samu bunkasa dabarun shi bayan da masana suka yi abubuwan da suka kamata, sai kuma ci gaban fasaha da abin ya canza yadda ake tafiyar da lamari a gargajiyance shekarun baya.Daga cikin dabarun koyarwa na zamani kamar koyarwa ta hadin kai na kungiya, koyarwa wadda aka tsara yadda za ta kasance,wadanda ake ganin za su iya daina yin karatu, karatu ta hanyar aikawa da kayan karatun, samun canji na koyo akan yadda masu koyon ke bukata, da kuma sauran makamantansu (Al-Kaisi, 2015).
In ana son dabarun koyarwa su kasance ingantattu saboda a cimma dalilan da suka sa aka kirkirosu wato inganta lamarin koyo dole ne a zabo su,ta hanyar yin la’akari da bin ka’idojin da aka shimfida kamar yadda suke (Ahmad, 2005).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp