Mazauna Jihar Sakkwato sun bayyana godiyarsu ga shugaba Bola Tinubu bisa namijin kokari don inganta tsaro a yankin ta hanyar ƙaddamar da gagarumin aikin kawar da ‘yan bindiga.
A jiya Lahadi, mazauna daban-daban sun tattauna da ‘yan jarida, suna yabawa kokarin Gwamnatin Tarayya wajen magance rashin tsaron da ake fama da shi a jihar.
- An Yi Garkuwa Da Sarkin Gobir Da Wasu Mutane 5 A Sokoto
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Malam Garba Mailambu, wani ɗan kasuwa a yankin, ya bayyana murna kan yadda gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi wajen kawar da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma, yana mai cewa irin wannan mataki ya kamata a ɗauka tun da wuri. Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi aikinsu yadda ya kamata tare da kira ga mazauna su ba wa sojoji goyon baya.
Dr. Habibu Ahmed Mada na Jami’ar Usman Danfodio ya yaba da umarnin kwanan nan na Ministan harkokin tsaro, Bello Matawalle, yana mai bayyana shi a matsayin babban matakin da zai kawo sauyi. Ya jaddada nasarar da Matawalle ya samu a baya wajen yaƙi da ‘yan tawaye a yankin, kuma ya nuna gamsuwarsa da jagorancinsa.
Wasu ƴan garin, kamar Mr. Shehu Haruna, sun goyi bayan kokarin Gwamnatin Tarayya, musamman suna kira ga Minista Matawalle da ya ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ‘yan bindiga da shugabansu, Bello Turji. Haruna ya jaddada muhimmancin dawo da tsaro domin mutane su koma gonakinsu kuma su samu ‘yancin zirga-zirga.