Matatar man Dangote, ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan.
Wani jami’in gudanarwar matatar ne ya bayyana haka a ranar Litinin.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗansanda Da Wani A Sakkwato
- Hadin Gwiwa Ce Tsakanin Sin da Afirka Ba Mulkin Mallaka ba
Matatar da darajarta ta kai dala biliyan 20, ta fara aiki ne a watan Janairu tare da samar da kayayyakin da suka hada da man jiragen sama.
Ita dai matatar mai fitar da ganganr mai 650,000 a kowace rana kuma mafi girma a Afirka an yi alkawarin za ta saukaka tsadar mai da kuma dogaro da man da ake shigowa da shi daga kasashen waje.
“Muna gwada samfurin (man fetur) kuma daga baya zai fara kwarara cikin tankunan da ake samarwa,” in ji Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin Dangote.
Sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da man fetur din zai fara shiga kasuwanni ba.
Edwin, ya ce kamfanin mai na kasa (NNPC), kadai za su sayar wa man fetur.
“Idan har kuma babu wanda ke saya, za mu fitar da shi zuwa kasashen waje kamar yadda muke fitar da man jirage da dizal,” in ji shi.