Kocin rikon kwarya na Super Eagles, Austin Eguavoen ya karyata ikirarin da ake yi na cewa ya nemi mukamin kocin na wucin gadi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, a baya-bayan nan, Eguavoen ya jaddada cewa nadin nasa ba wai wani kokari ko wani tasiri na kansa ba ne, illa yardar Allah.
“Ni memba ne na tarayya, ina aiki a matsayin daraktan fasaha na hukumar kwallon kafa ta Nijeriya,” in ji shi.
“Lokacin da irin wannan yanayi ya zo kuma idan an kira ku, ba za ku iya cewa a’a ba aiki ne da na yi aiki ne da ke karkashin alhakina.”
Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF), ta tabbatar da nadin Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya na Super Eagles a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika (AFCON) da Jamhuriyar Benin da Rwanda.
An yanke shawarar ne bayan tattaunawa da kocin Jamus Bruno Labbadia ya wargaje.
Eguavoen, mai shekaru 59, wanda ya yi aiki a matsayin daraktan fasaha na tawagar tun daga shekarar 2020, zai dauki dan lokaci yayin wannan hutun na kasa da kasa.
Shahararren dan wasan na Super Eagles, dai ba bakon mutum ba ne a wannan matsayi, inda a baya ya taba horar da ‘yan wasan kasar a matakai uku daban-daban, na baya-bayan nan.
A shekarar 2021ya jagoranci kungiyar a gasar AFCON bayan korar da aka yi wa tsohon kocin tawagar, Gernot Rohr.