Akalla mutane tara sun rasa rayukansu, yayin da mutum daya ya samu munanan raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Kongo da ke Æ™aramar hukumar Bokkos a Jihar Filato.Â
Wata majiya da ta nemi a sakaye sunansa, ya ce wanda aka jikkata na cikin mawuyacin hali a yanzu ƙarƙashin kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba.
- A Gaggauta Janye Ƙara Farashin Man Fetur – NLC Ga Gwamnatin TarayyaÂ
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 8 A Borno Da Yobe
Ya Æ™ara da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na dare, jim kadan bayan rufe kasuwar wanda akasarin jama’a sun watse daga harabar kasuwar saura mutane kadan suka rage.
Wannan lamarin dai ya sake haifar da fargaba da zaman dar-dar a yankin duba da yadda al’ummomin ƙaramar hukumar ta Bokkos a ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, yayin tattara wannan rahoto bai samu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp