Za a gudanar da taron ’yan kasuwan Sin da Afirka karo na 8 a ran 6 ga watan nan, kasancewar taron wani muhimmin sashi na taron kolin dandalin tattauna kan hadin gwiwar Sin da Afirka na 2024 wato FOCAC, ya jawo hankalin wakilai 408 daga kasashen Afirka 48, ’yan kasuwan bangarorin biyu za su tattauna kan yadda za su gaggauta hadin gwiwarsu a sabbin sha’anoni.
Taron na wannan karo zai gayyato wakilan Sin da Afirka 12 don musayar dabaru da fasahohinsu a bangaren gaggauta hadewar tsare-tsaren samar da kayayyaki da ingiza sabbin sana’o’i, da kuma tattauna damammakin da manufofin da taron kolin FOCAC zai samar.
- Me Ya Sa Dandalin FOCAC Ke Samun Karbuwa A Tsakanin Al’ummar Nahiyar Afrika?
- Xi: Sin Da Afirka Sun Zamo Sassa Na Farko Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya
Mataimakin shugaban kwamitin gaggauta bunkasuwar cinikayyar kasa da kasa na kasar Sin Zhang Shaogang ya yi bayani a cibiyar yada labarai ta FOCAC a yammacin jiya Talata cewa, Sin ita ce kasa daya tak a duniya da ta mallaki dukkan nau’o’in masana’antu na duniya, Sin da Afirka na bukatar juna sosai a bangaren tsarin samar da kayayyaki, hakan zai samar da makoma mai haske kan hadin gwiwarsu. Ban da wannan kuma, Sin na gaggauta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, a nasa bangare kuwa, Afirka ta dukufa kan bullo da wata hanya ta zamani na samun bunkasuwa ta dogaro da kai.
Kazalika, Sin da Afirka na da boyayyen karfi wajen hadin gwiwarsu a fannin tattalin arzikin yanar gizo da raya tattalin arziki tare da kiyaye muhalli da na’urori masu kwaikwayon tunanin dan adam wato AI da sauransu, ana fatan ’yan kasuwan Sin da Afirka za su daukaka hadin gwiwarsu a wasu sabbin sana’o’i da ma ingiza bunkasuwarsu. (Amina Xu)