Ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai kan al’ummar Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, wasu ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun afkawa al’umma a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka kaddamar da ta’addancin da ya kai ga kashe dimbin mazauna garin Mafa.
- Majalisa Ta Nemi Hukumar Shari’a Ta Binciki Sheikh Gadon-Ƙaya Kan Zargin Auren Jinsi A Bauchi
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Fannin Sabbin Makamashi Ya Samar Da Mafita Ta Tabbatar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Afirka
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun afkawa kauyen ne a kan babura da tsakar daren Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi, hakan ya yi sanadin mutuwar mazauna kauyen ciki har da kananan yara da tsofaffi.
Sanarwar wacce ta fito daga ofishin Jakadancin kasar, ta jaddada yadda Masarautar Saudiyya ke adawa da duk wani nau’in tashe-tashen hankula, ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
Sannan ta mika sakon ta’aziyyar Masarautar tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, gwamnatin Nijeriya da al’ummar jihar Yobe.
In ba a manta ba, mun rahoto muka yadda ‘yan ta’addan suka kashe mutanen da ba a tantance adadinsu ba, tare da kona gidaje da makarantu da dai sauransu.
A ranar Talatar da ta gabata ne aka binne gawarwakin wadanda aka kashe a unguwar Babbangida da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar.
Hukumomin tsaro sun ce, ana ci gaba da kokarin ceto wadanda suka bata sakamakon mummunan harin.